Kwankwaso Ya Yi Gargadi kan Tsaro yayin da Ganduje ke Shirin Kafa Hisbah a Kano
- Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna damuwa kan yadda tsaro ke kara tabarbarewa a sassan kasar nan a halin yanzu
- Ya ce gwamnati ta kasa iya dakile yaduwar miyagun makamai, ta’addanci da rikice-rikicen kabilanci a Najeriya
- Jagoran jam'iyyar NNPP ya yi gargadi da cewa siyasa da tashe-tashen hankali suna kara raunana hadin kan kasa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Tsohon Gwamnan Kano kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya magantu kan manyan matsalolin tsaro da ke kara ta’azzara a fadin kasar nan.
Kwankwaso, wanda ya taba zama ministan tsaro, ya nuna damuwa kan yadda al’amuran ‘yan daba, ta’addanci, rigingimun kabilanci da yaduwar makamai ke ci gaba da zama barazana a Najeriya.

Source: Facebook
Legit Hausa ta gano cewa Kwankwaso ya yi wannan furuci ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a yau Litinin.
Maganar Kwankwaso kan yaduwar makamai
Rabiu Kwankwaso ya ce alamar da ke nuna cewa gwamnati ta gaza, ita ce yadda take barin jihohi su rika kafa kungiyoyin sa-kai ba tare da cikakken horo ba, abin da ya kara yaduwar makamai a hannun jama’a.
Kwankwaso ya bayyana cewa:
“Abin takaici, alamu na nuna gwamnatin tarayya ta gaza. Wannan ya bayyana a yadda ta amince wa jihohi su kafa kungiyoyin sa-kai, duk da rashin ingantaccen horo.”
Rabiu Kwankwaso ya ce irin wannan tsarin ya taimaka wa yaduwar manyan makamai da kananan bindigogi a cikin al’umma.
Ya kara da cewa wannan halin da ake ciki ya ba wa wasu ‘yan siyasa damar kafa kungiyoyinsu na musamman domin cimma muradunsu, abin da ke kara dagula tsaro.
A cewarsa:
“Mafi muni, akwai wadanda suka fara amfani da wannan dama wajen kafa rundunonin kansu, kamar yadda wasu ‘yan siyasa ke yi. Wannan yana kara tada hankalin kasa.”
Kwankwaso ya ce rikicin kabilanci na karuwa
Tsohon ministan ya kuma nuna damuwa kan yadda ake ta samun karin rikice-rikice da tsangwama da ke tasowa bisa kabilanci ko bambancin yanki.
Ya ce ana iya tsare mutane, ko cin zarafinsu, musamman wadanda ke fitowa daga wasu yankuna na kasar nan a yanzu.
Daily Trust ta rahoto ya ce:
“Wannan matsalar tana kara tsananta ne saboda cin zarafi, tsangwama da kalaman kiyayya da ake yadawa a kafafen sada zumunta. Irin wadannan dabi’u suna barazana ga dunkulewar kasa da hadin kai.”
Kwankwaso ya bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki mataki cikin gaggawa domin dakile wannan yanayi kafin ya rikide zuwa wani hali mafi muni.
Kwankwaso ya taya Janar CG Musa murna
Sai dai duk da wannan damuwa, ya taya Janar Christopher Gwabin Musa murnar nada shi a matsayin ministan tsaro, yana mai cewa idan an ba shi goyon bayan da ya dace, zai iya kawo canji mai amfani ga kasar.

Source: Twitter
A cewarsa:
“Ina da yakinin cewa idan aka ba shi goyon bayan da ya dace, yana da kwarewa da gogewa da za su iya dawo da tsaro da zaman lafiya a kasa.”
Abdullahi Ganduje zai kafa Hisbah a Kano
A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce zai kafa sabuwar Hisbah a jihar Kano.
Biyo baya bayanin da Ganduje ya yi, an fitar da fom domin ba jama'a damar neman shiga aikin sabuwar Hisbah a jihar.
Shugabannin da suka jagoranci kaddamar da fom din sun bayyana cewa za su yi aiki ne domin kawo zaman lafiya da cigaba.
Asali: Legit.ng


