Wata Sabuwa: Ganduje Ya Fara Raba Fom din Shiga Aikin Sabuwar Hisbah a Kano
- An kaddamar da rabon takardun neman shiga sabuwar Hisbah a Kano, wacce za a kafa karkashin Gidauniyar Ganduje
- Jagororin sabuwar kungiyar sun ce hukumar da za su kafa ba ta gwamnati ba ce, aiki ne na sa-kai domin hidimar addini
- Wani lauya ya soki wannan yunkuri, yana kira ga hukumar DSS da ta kama masu yada fom din saboda zargin tada hankali
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - An kaddamar da fitar da takardun neman aiki a sabuwar kungiyar Hisbah mai zaman kanta da aka kafa karkashin Gidauniyar Ganduje a Kano.
An gudanar da taron ne a birnin Kano, inda aka bayyana cewa kungiyar za ta yi aiki ne domin hidimar addini da gudanar da ayyukan jinƙai.

Source: Facebook
Leadership ta rahoto cewa shirin ya samu jagorancin fitaccen jigon jam’iyyar APC, Hon. Baffa Babba Dan Agundi, tare da tsohon kwamandan Hisbah na jihar Kano, Sheikh Harun Ibn Sina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matakin ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a, inda wasu ke ganin hakan na iya haifar da rikici ko rarrabuwar kawuna a Kano.
Ganduje ya fitar da fom din Hisbah a Kano
Sheikh Harun Ibn Sina, wanda yake jagorantar shirin, ya bayyana cewa kafa Hisbah mai zaman kanta na da nufin samar da wata sabuwar hanya ga mutanen da aka dakatar daga aikin Hisbah ta gwamnati.
A cewarsa, kusan mutane 12,000 ne suka rasa mukamansu a baya, kuma wannan tsari zai ba su damar ci gaba da hidimar al’umma.
Ya ce:
“Wannan ba hukuma ba ce ta gwamnati. Kungiya ce ta sa-kai da muka kirkiro domin neman falalar Allah. Ba mu adawa da Hisbah ta gwamnati.”
Ibn Sina ya nanata cewa kungiyar ba ta da wata manufa ta siyasa ko rikici, sai dai hidima da tsare tarbiyya bisa koyarwar addinin Musulunci.
Fargabar da jama’a suka bayyana a Kano
Duk da bayanan masu jagorancin kungiyar, rahotanni sun nuna cewa akwai fargaba a Kano, musamman daga wadanda ke kallon wannan mataki a matsayin wani sabon salo na siyasa q jihar.
Wasu mazauna Kano sun bayyana damuwarsu cewa kafa wata Hisbah ta dabam na iya haifar da rikice-rikicen siyasa.

Source: Facebook
Lauya ya soki Ganduje kan kafa Hisbah
Wani lauya a Najeriya, Hamza Nuhu Dantani, ya yi suka kan kafa sabuwar Hisbah da Gidauniyar Abdullahi Ganduje za ta yi.
A sakon da ya wallafa a Facebook, lauyan ya ce wannan yunkuri na iya haifar da rikici ko kuma amfani da kungiyar wajen tada hankalin jama’a.
Ya ce:
“Yunkurin rabar da fom na shiga Hisbah mai zaman kanta babu abin da ya raba shi da ta’addanci da kuma shirin tada hankalin jama’a a Kano. Ya kamata DSS ta kama duk wanda ke raba wannan fom din.”
Hisbah: Bashir Ahmad ya soki Ganduje
A wani labarin, kun ji cewa tsohon hadimin marigayi shugaba Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya soki Abdullahi Umar Ganduje kan kafa Hisbah.
Bashir Ahmad ya ce yunkurin kafa wata hukumar Hisbah a Kano bayan wacce ke karkashin gwamnatin jihar zai iya haifar da matsala.
Ya bayyana shakku game da dalilan da Ganduje ya bayar tare da cewa samar da tsaro a Kano yana karkashin gwamnatin jihar ne ba wani mutum ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


