Yadda Tinubu Ya Tura Sojoji Benin Suka Fatattaki Masu Son Juyin Mulki
- Fadar shugaban kasa ta ce gwamnatin Binin ta nemi taimakon gaggawar Najeriya bayan wasu sojoji sun yi yunkurin kifar da gwamnatin Patrice Talon
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci jiragen yakin NAF su shiga Benin domin kwace tashar Talabijin da kuma sansanin soja da dakarun suka mamaye
- Biyo bayan lamarin, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yaba da yadda dakarun Najeriya suka yi aiki wajen kare dimokuradiyya a kasar Benin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jinjinawa rundunar sojan Najeriya kan matakin gaggawa da ta dauka wajen kare dimokuraɗiyyar ƙasar Binin bayan yunkurin juyin mulki da aka yi a safiyar Lahadi, 7, Disamba, 2025.
An ce yunkurin juyin mulkin ya girgiza makwabciyar Najeriya wacce ta shafe shekaru 35 tana tafiya kan tsarin dimokuradiyya ba tare da tangarda ba.

Source: Twitter
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya wallafa a shafinsa na X cewa shi da kansa ya ba dakarun Najeriya izinin shiga Benin bayan taimakon da kasar ta nema.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojojin Najeriya sun kai dauki Benin
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin Binin ce ta nemi taimakon Najeriya, inda ta tura bukatu biyu ta hanyar ma’aikatar harkokin wajen ta, tana neman tallafin gaggawa a sararin samaniya da kuma a ƙasa domin kare al’amuran gwamnati.
Bisa bukatar farko da gwamnatin Benin ta aike, shugaba Tinubu ya umarci jiragen yakin Najeriya su shiga ƙasar domin kwace sararin samaniyar Binin da ’yan juyin mulkin suka mamaye.
Jiragen yakin sun taimaka wajen fatattakar sojojin Colonel Pascal Tigri, wanda ya jagoranci yunkurin juyin mulki a kasar.
A karo na biyu, gwamnatin Binin ta sake bukatar Najeriya ta tura karin jirage domin sa ido da mayar da martani bisa tsarin da rundunar Benin za ta jagoranta.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta dauki matakai 3 bayan sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Benin
Bayo Onanuga ya wallafa a X cewa hakan ya ba da damar tsare tashoshin gwamnati da kuma dakile yaduwar tawaye zuwa wasu yankuna a fadin kasar.
Najeriya ta tura sojojin kasa Benin
Baya ga taimakon jiragen sama, gwamnatin Benin ta nemi sojojin ƙasa na Najeriya domin wasu ayyuka na musamman da ta amince da su.
Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya tabbatar da cewa an cika dukkan bukatun da Benin ta nema, kuma dakarun Najeriya sun isa wuraren da aka tura su.

Source: Twitter
Tinubu ya yabawa rundunar soja
A cikin jawabin sa, Shugaba Tinubu ya jinjinawa jarumtakar rundunar sojojin Najeriya, yana mai cewa sun tsaya wajen kare dimokuraɗiyya kamar yadda ake bukata.
Ya ce matakin da aka dauka ya dace da ka’idar ECOWAS kan mulki da kyautata tsarin dimokuraɗiyya tun daga 1999.
Ya kara da cewa Najeriya za ta ci gaba da goyon bayan gwamnati da al’ummar Benin domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban yankin.
Tinubu ya taya Tanko Yakasai murna
A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya dattijon Arewa, Tanko Yakasai murnar cika shekara 100.
Bola Tinubu ya bayyana cewa Tanko Yakasai ya bayar da gudumawa a fannoni da dama a tsawon rayuwar da ya yi.
Shugaban kasar ya kara da cewa dattijon ya taka rawa wajen fafutukar samawa Najeriya 'yancin kai daga hannun turawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
