‘Kisan Kiristoci’: Tawagar Amurka Ta Shigo Najeriya, Ta Yi Magana da Ribadu

‘Kisan Kiristoci’: Tawagar Amurka Ta Shigo Najeriya, Ta Yi Magana da Ribadu

  • Tawagar majalisar dokokin Amurka ta shiga Najeriya yayin da ake ci gaba da zargin kisan Kiristoci wanda ya tayar da kura
  • Mai taimakawa shugaban kasa kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu shi ya karɓi tawagar majalisar a Abuja domin ci gaba da tattaunawar tsaro
  • Sun tattauna kan haɗin gwiwar yaki da ta’addanci, zaman lafiyar yankin da kuma ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu, ya karbi tawaga ta musamman daga Amurka.

Ribadu ya bayyana a ranar Lahadi 7 ga watan Disambar 2025 cewa ya karɓi tawagar ’yan majalisar dokokin Amurka a Abuja.

Ribadu ya gana da tawagar yan majalisar Amurka a Najeriya
Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu. Hoto: Nuhu Ribadu.
Source: Facebook

Abin da aka tattauna da Ribadu, tawagar Amurka

Hakan na cikin wani rubutu da ya yi a shafin Facebook a yau Lahadi kamar yadda waiklin Legit Hausa ya leko.

Kara karanta wannan

Shari'ar Musulunci: MURIC ta kalubalanci Amurka, ta faɗi abin da Musulmi za su yi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ganawar wani ɓangare na tattaunawar tsaro da ke gudana tsakanin ƙasashen biyu.

Ribadu ya ce wannan ziyara ta biyo bayan tattaunawar da suka yi tun a birnin Washington, DC, kan abubuwan tsaro da suke bai wa juna muhimmanci.

A cewarsa:

“Da safiyar yau na karɓi tawagar majalisar dokokin Amurka da ke ziyarar tantance gaskiya a Najeriya, bayan tattaunawa da suka gabata a Washington kan abubuwan tsaro da muke da sha’awa tare.”

Ya ƙara da cewa jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills, ya halarci ganawar, wanda ya nuna muhimmancin da ƙasashen biyu ke bai wa wannan tattaunawa.

Tawagar Amurka ta zo Najeriya, ta gana da Ribadu
Nuhu Ribadu yayin ganawa da tawagar majalisar Amurka. Hoto: Nuhu Ribadu.
Source: Facebook

Ribadu ya yi karin haske kan tattaunawar

Ribadu ya bayyana cewa tattaunawar ta mayar da hankali kan “haɗin gwiwar yaƙi da ta’addanci, zaman lafiyar yankin,” da kuma hanyoyin zurfafa haɗin tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.

Ya ce yana sa ran wannan tattaunawa za ta ƙara aminci, haɗin kai da jajircewa wajen zaman lafiya da tsaro.

Kara karanta wannan

Farin jinin Matawalle ya fadada, 'yan Kudu sun roki Tinubu game da kujerarsa

Ganawar ta gudana ne a daidai lokacin da ake fuskantar matsin lamba a diflomasiyya, bayan shugaban Amurka Donald Trump ya sake maida Najeriya cikin jerin 'ƙasashen masu babbar matsala'.

Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da zargin, tana mai cewa matsalolin tsaro a ƙasar ba su da alaƙa da addini, domin suna shafar al’umma daga dukkan bangarori.

Yayin da matsin lamba ke ƙaruwa, Gwamnatin Najeriya ta ci gaba da neman taimakon diflomasiyya da tsaro daga ƙasashe daban-daban.

A ranar 20 ga Nuwamba, ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya karɓi Ribadu a Pentagon domin tattaunawa kan dabarun haɗin gwiwa wajen magance rikicin tsaro da ke addabar ƙasar.

An taso Ribadu a gaba sai ya yi murabus

An ji cewa an taso Shugaba Bola Tinubu ya gaba da sauya mai ba shi shawara kan harkokin tsaro a Najeriya, Malam Nuhu Ribadu.

Sanata Francis Fadahunsi ya bukaci Tinubu ya nada tsohon hafsan soja a matsayin NSA, yana cewa hakan ne kawai zai tabbatar tsaro.

Fadahunsi ya yaba da nadin tsohon hafsan tsaro, Christopher Musa, kuma ya ce lokaci ya yi da ake bukatar ƙwararrun sojoji.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.