Me Ake Kullawa: Atiku Ya Gana da Tsohon Shugaban Kasa Jonathan

Me Ake Kullawa: Atiku Ya Gana da Tsohon Shugaban Kasa Jonathan

  • Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya gana da tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan
  • Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban kasar ne a gidansa da ke Abuja, 'yan kwanaki kadan bayan ya dawo daga aikin sa ido kan zaben kasar Guinea Bissau
  • Ziyarar da tsohon mataimakin shugaban kasar ya kai wa Goodluck Jonathan na zuwa ne bayan ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC watanni bayan ya bar PDP

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban kasar ne a gidansa da ke Abuja a ranar Asabar, 6 ga watan Disamban 2025.

Atiku ya ziyarci Goodluck Jonathan
Atiku Abubakar tare da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan Hoto: @atiku
Source: Twitter

Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a wata wallafa tare da hotunan ganawar ta su a shafinsa na X a ranar Lahadi, 7 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

PDP ta manta da adawa, ta koma neman taimako wajen Shugaba Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jonathan ya je kasar Guinea Bissau

Ziyarar ita ce ta farko tun bayan dawowar Jonathan daga aikin sa ido kan zaben da aka gudanar a Guinea-Bissau.

Tsohon shugaban kasar dai yana daga cikin tawagar WAEF da ta tafi duba zaɓukan da aka gudanar a ranar 23, Nuwamba, 2025.

Sai dai, Jonathan da sauran daruruwan masu sa ido sun makale a kasar ta yankin Afrika ta Yamma bayan sojoji sun sanar da kifar da gwamnatin Shugaba Umaro Sissoko Embalo, kafin sanar da zaben shugaban kasa.

Sojojin da suka aiwatar da juyin mulkin sun bayyana cewa sun samu “cikakken iko” bayan manyan ‘yan takara biyu sun yi iƙirarin nasara.

Bayan dawowa gida Najeriya, Jonathan ya bayyana cewa juyin mulkin ya fi masa zafi fiye da ranar da ya kira Muhammadu Buhari ya taya shi murna bayan shan kaye a zaben 2015.

Atiku ya hadu da Jonathan

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ministan tsaro, Mohammed Badaru ya yi murabus

“Abin farin ciki ne sake haɗuwa da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan jiya da yamma, bayan dawowarsa daga Guinea-Bissau.”

- Atiku Abubakar

Jonathan, wanda ya yi mulki daga 2010 zuwa 2015, ya yi rashin nasara a yunkurin sake tsayawa takara a 2015 inda marigayi Muhammadu Buhari ya kayar da shi.

Atiku ya gana da Shugaba Goodluck Jonathan
Goodluck Jonathan tare da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan Hoto: @atiku
Source: Twitter

Ziyarar ta biyo bayan sauya shekar da Atiku ya yi zuwa jam’iyyar ADC, watanni bayan ya fice daga PDP.

Atiku ya shiga ADC ne bayan ya yi murabus daga PDP, yana mai cewa jam’iyyar ta kauce daga ka’idoji da manufofin da mutanen da suka kafa ta suka shimfiɗa.

Ana hasashen cewa Atiku na iya zama ɗan takarar shugaban kasa na ADC a zaben 2027.

Jonathan ya fadi dalilin ja baya da siyasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya yi magana kan dalilin da ya sa ya ja baya daga shiga harkokin siyasa.

Jonathan ya bayyana cewa rawar da yake takawa a matsayin mamba a kungiyar West African Elders Forum (WAEF) na bukatar tsantsar rashin nuna goyon baya ga wani bangare.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da babban hafsan tsaron Najeriya da ya kora daga aiki

Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa zama mamba na WAEF yana zuwa ne da sharadi ɗaya mai tsauri, ba za ka ci gaba da shiga siyasa ta jam’iyya ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng