Ya Matso Kusa da Najeriya: Sojoji Sun Sake Juyin Mulki a Afrika ta Yamma
- Ana fargabar sojoji sun sake yin juyin mulki a wata kasar Afirka bayan kifar da gwamnatin Guinea-Bissau a kwanakin baya
- Majiyoyi sun ce sojoji sun bayyana a gidan talabijin na Benin inda suka sanar da rushe gwamnatin kasar ba tare da bata lokaci ba
- Alamu sun nuna wannan juyin mulki ne da ya kifar da Shugaba Patrice Talon wanda ke da makwabtaka da kasar Najeriya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Porto-Novo, Benin - Wani rukuni na sojoji sun bayyana a gidan talabijin na gwamnati a Jamhuriyar Benin, inda suka sanar da rushe gwamnati.
Wannan lamari da ake ganin na kama da juyin mulki ya tayar da hankula ganin yadda rushe dimokuraɗiyya ke kara yawa.

Source: Getty Images
Sojoji sun karbi iko a Jamhuriyar Benin
Rahoton Aljazeera ya tabbatar da cewa sojojin sun sanar hakan ne a ranar Lahadi 7 ga watan Disambar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun bayyana cewa sun hambarar da Shugaba Patrice Talon, wanda yake mulki tun shekarar 2016, lamarin da ya tada hankulan jama’a.
Ana jiran ƙarin bayani kan wannan sabon juyin mulki, yayin da lamarin ya jefa al’ummar ƙasar cikin fargaba da rashin tabbas game da makomar Benin.

Source: Facebook
Bayanai kan yadda tashin hankalin ya fara
A cewar France24, tashin hankalin ya fara ne da sassafe lokacin da aka kai hukumar harin makami a gidan shugaban ƙasa Patrice Talon da ke Porto-Novo.
Rahotanni sun ce Laftanar-Kanal Pascal Tigri ne ya jagoranci harin, tare da sojojin da ke biyayya gare shi, inda daga baya suka kwace ikon gidan talabijin na ƙasa.
Bidiyon da aka nuna a talabijin na gwamnati ya nuna sojoji cikin kayansu suna karanta sanarwa, suna ikirarin cewa sun ɗauki mulki ne “don dawo da oda”.
Babu inda aka samu labarin inda Talon ya ke a lokacin, sai dai Ofishin Jakadancin Faransa ya ce an ji karar harbe-harbe a sansanin "Guezo” kusa da wurin zaman shugaban ƙasa.
Gargadin Faransa ta yi wa yan kasarta
Ofishin ya shawarci ‘yan ƙasar Faransa da su zauna a cikin gidajensu saboda tsaro har zuwa lokacin da lamura za su dawo daidai kamar yadda suke a baya.
Benin, wacce ake kira Jamhuriyar Benin tsohuwar Masarautar Dahomey, ƙasa ce a Yammacin Afirka da ke iyaka da Togo a Yamma.
Har ila yau, tana da kusanci da NajeriyaGta gabas, Burkina Faso a arewa maso Yamma, sannan Niger a Arewa maso Gabas.
An yi juyin mulki a Guinea-Bissau
A baya, kun ji cewa sojojin Guinea-Bissau sun sanar da cewa sun karɓi cikakken iko a ƙasar bayan kwanaki uku kacal da zaɓen ’yan majalisa da na shugaban ƙasa.
Rahotanni sun nuna cewa tun da safiyar ranar Laraba 26 ga watan Nuwambar 2025, aka ji karar harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa, sojoji sun mamaye manyan hanyoyi.
Dakarun sojin sun karanta sanarwa daga Babban Hedikwatar Soji a Bissau, babban birnin kasar bayan sun gama kwace iko da kuma kama shugaban kasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

