Gwamna Ya ba Mawaƙin Yabo Makaho Jarin N100m, Ya Ware Masa Albashin N1m

Gwamna Ya ba Mawaƙin Yabo Makaho Jarin N100m, Ya Ware Masa Albashin N1m

  • Gwamna Umo Eno ya tallafa wa mawakin makaho fili, gida, da jarin miliyoyi domin karfafa dogaro da kai a Akwa Ibom
  • Gwamnan ya ce za su gina masa gida mai ɗakuna huɗu, su samar masa da shagon aiki, tare da ba shi alawus duk wata
  • Eno ya jaddada cewa Chris Vic ya zama abin koyi ga masu nakasa, yana nuna yabon Allah yana yiwuwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Uyo, Akwa Ibom - Gwamna Umo Eno ya sake yin abin da ya saba na taimakawa masu bukata ta musamman domin ci gaba da dogaro da kansu.

Gwamnan ya ba wani mawakin yabo da ya kasance makaho jarin miliyoyin Naira domin ci gaba da harkokin wakokinsa ba tare da matsala ba.

Gwamna ya yi abin alheri ga mawakin makaho
Gwamna Umo Eno da makahon mawakin yabo. Hoto: @_PastorUmoEno.
Source: Twitter

Alwashin da gwamna yi ga masu nakasa

Kara karanta wannan

Albishir da ministan tsaro ya fara yi ga 'yan Najeriya bayan shiga ofis a Abuja

Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga shafin gwamnan na X wanda ya wallafa a yau Lahadi 7 ga watan Disambar 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin rubutunsa, Gwamna Eno ya ce zai ci gaba da tallafawa masu bukata ta musamman domin dogaro da kansu.

Ya yabawa makahon yadda ya fita daban da sauran masu lalura irin tasa inda ya ya ba shi jarin N100m da kuma ba shi fili a birnin Uyo.

Ya rubuta cewa:

"Na umurci Kwamishina da ya ware filin a Uyo domin Chris Vic, kuma zan sanya hannu kan takardar mallakar filin a mako mai zuwa."
"Haka kuma, za mu gina masa gida mai ɗakuna huɗu, sannan mu bayar da gudummawar Naira miliyan ɗari domin samun shagon rikodin wakokinsa, wannan ba ya cikin kuɗin filin da na ginin."
Gwamna ya shawarci masu nakasa ta musamman a Akwa Ibom
Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom. Hoto: Pastor Umo Eno.
Source: Facebook

Alkawarin da Gwamna ya yi ga makaho

Gwamna Eno ya kuma yi masa alkawarin ba shi albashi N1m duk wata har iya tsawon kasancewarsa a kan mulki.

" Bugu da ƙari, muddin ina ci gaba da zama Gwamna, zai rika karɓar alawus na wata-wata na Naira miliyan ɗaya."

Kara karanta wannan

'Abin da ka shuka': Kotu ta yanke wa matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya

- Umo Eno

Gwamna ya tunatar da masu nakasa su kasance kamar Chris domin tsayawa da kafafunsu inda ya shawarce su da su yi koyi da shi domin dogaro da kai.

Ya ji dadin yadda matashin mawakin duk da kasancewarsa makaho amma bai kashe zuciyarsa ba inda ya dukufa da wake irin na yabo.

Ya kara da cewa:

"Wannan ya zama tunatarwa gare mu cewa duk a cikin mawuyacin hali, Chris Vic ya nuna mana cewa yabon Allah yana yiwuwa a kowane yanayi.
"Ina kuma so shi da dukkan masu nakasa su sani cewa wannan gwamnati na kulawa da su."

Yadda Gwamna Eno ya sha tsangwama

Kun ki cewa Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, ya bayyana yadda aka yi masa ba’a yayin da yake kamfe na neman takarar gwamna.

Mai girma Gwamnan ya ce nuna masa wariya sosai saboda shi zabiya ne a yakin neman zaben 2023 a jihar Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

'Suna da manyan makamai,' Sheikh Gumi ya ce ana taimakon 'yan ta'adda daga ketare

Eno ya ce ya sha wahala tun yana yaro saboda halittasa, amma yau yana karrama masu irin wannan yanayi saboda nuna darajarsu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.