Gwamna Sokoto Ya Raka Takwaransa na Abia Ziyartar Nnamdi Kanu? An Ji Gaskiyar Zance

Gwamna Sokoto Ya Raka Takwaransa na Abia Ziyartar Nnamdi Kanu? An Ji Gaskiyar Zance

  • An yada wasu rahotanni masu cewa gwamnan jihar Sokoto ya raka takwaransa na Abia, ziyartar shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu
  • Gwamnatin Sokoto ta fito da gaggawa ta yi martani kan rahotannin masu cewa har da Gwamna Ahmed Aliyu aka ziyarci Kanu a gidan yari
  • Tuni gwamnatin Ahmed Aliyu bayyana cewa tabbas wakilan gwamnati sun tarbi Otti cikin mutuntawa yayin ziyarar da ya kawo jihar Sokoto

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ta yi martani kan rahotannin da ke cewa da Gwamna Ahmed aka ziyarci shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

Gwamnatin ta karyata rahotannin da ke cewa Gwamna Ahmed Aliyu ya raka takwaransa na Abia, Alex Otti, yayin ziyarar da ya kai wa Nnamdi Kanu, a gidan gyaran hali na Sokoto.

Gwamnan Sokoto ya musanta ziyartar Nnamdi Kanu
Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu, Nnamdi Kani da gwamnan Abia, Alex Otti Hoto: @Ahmedaliyuskt, @alexottiofr
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Abubakar Bawa, ya fitar a ranar Juma’a, 5 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

'Yan Biyafara sun taru sun harzuka bayan daure Nnamdi Kanu a Sokoto

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane martani gwamnatin Sokoto ta yi?

A cikin sanarwar gwamnatin ta musanta ikirarin cewa Gwamna Ahmed Aliyu ya raka Alex Otti zuwa wajen Kanu.

“Don kawar da shakku, Gwamna Ahmed Aliyu yana a kasar Saudiyya yana yin aikin Umrah a ranar 30 ga Nuwamba, 2025, lokacin da Dr. Otti ya ziyarci jihar Sokoto."

- Abubakar Bawa

Sanarwar ta ce wasu kwamishinoni da mashawarta ne suka tarbi Gwamna Otti a filin jirgin Sama na Sultan Abubakar III, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.

Daga nan sun raka shi zuwa fadar gwamnatin jihar Sakkwato, inda aka yi masa kyakkyawar tarba kamar yadda ake yi wa kowane gwamnan da ke ziyara.

“Kamar yadda ku ka sani, mutanen Sokoto mutane ne masu karamci. Muna mutunta baƙi ba tare da la’akari da yare ko addini ba."

- Abubakar Bawa

Gwamnan jihar Sokoto na son zaman lafiya

Sanarwar ta kara jaddada matsayin Gwamna Ahmed Aliyu na jajircewa kan ci gaban Najeriya da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

'Ina cikin aminci a Najeriya': Tsohon Firayim ministan Birtaniya kan tsaro

“Gwamnatin jihar Sokoto tana jaddada cewa Gwamna Ahmed Aliyu yana girmama doka da oda, yana da kishin Najeriya, kuma mutum ne mai son zaman lafiya da bin doka.”

- Abubakar Bawa

Gwamnan Sokoto ya musanta ziyartar Nnamdi Kanu a gidan gyaran hali
Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu Hoto: @Ahmedaliyuskt
Source: Facebook

Gwamna Otti ya ziyarci Kanu a kurkukun Sokoto

Wannan karin bayani ya biyo bayan ce-ce-ku-ce kan ziyarar da Gwamna Otti ya kai wa Nnamdi Kanu, ziyarar da kungiyar IPOB ta kira “mai tarihi” kuma “abin mamaki.”

Gwamnan jihar Abia ya je tare da kanin Nnamdi Kanu, Emmanuel Kanu, kwamishinan Shari’a, Ikechukwu Uwanna (SAN); da mashawarcinsa kan harkokin yada labarai, Ferdinand Ekeoma.

A ranar 20 ga Nuwamba, 2025, kotu ta yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin daurin rai da rai bayan ta same shi da laifin ta’addanci da wasu laifuffuka daban-daban.

Nnamdi Kanu na son dauke shi daga Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa jagoran kungiyar 'yan aware ta IPOB, Nnamdi Kamu, ya mika sabuwar bukata a gaban kotu.

Mazi Nnamdi Kanu ya ya shigar da korafi a gaban babbar kptun da ke Abuja yana neman a cire shi daga gidan yarin Sokoto.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Nnamdi Kanu ya fadi dalilin neman ɗauke shi daga gidan yarin Sokoto

A cikin buƙatar da ya sanya hannu da kansa, Kanu ya ce zaman sa a Sokoto za ta hana shi yin ingantaccen shiri na daukaka kara.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng