Malami: Tsohon Ministan Buhari Ya Dau Zafi bayan an Zarge Shi da Daukar Nauyin Ta'addanci
- Tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami, ya yi tsokaci bayan an ambaci sunansa cikin mutanen da ake zargi da daukar nauyin ta'addanci
- Abubakar Malami ya bayyana cewa ko sau daya ba a taba gayyatarsa a ciki ko wajen Najeriya kan batun da ya shafi daukar nauyin ta'addanci ba
- Malami wanda ya kasance babban lauyan gwamnati ya bayyana manufar da mutanen da ke yada zargin daukar nauyin ta'addancin ke son cimmawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya yi magana kan zargin daukar nauyin ta'addanci.
Abubakar Malami ya karyata zarge-zargen da ke danganta shi da daukar nauyin ta’addanci, yana mai bayyana su a matsayin na karya, na yaudara kuma na siyasa.

Source: Twitter
Tsohon Ministan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Juma’a, 5 ga watan Disamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ambaci Malami kan zargin daukar nauyin ta'addanci
Malami ya ce hankalinsa ya kai kan wani rahoto da ke kokarin nuna cewa shi da wasu mutane suna da alaka da wasu da aka bayyana su a matsayin masu alaka da ta’addanci ko masu taimakawa ‘yan ta’adda.
Rahoton ya ambaci sunansa yana danganta shi da zargin daukar nauyin ta’addanci da kuma “alaka” da wasu da ake zargi da ta'addanci da daukar nauyinsa.
Me Malami ya ce kan daukar nauyin ta'addanci?
Sai dai tsohon ministan ya bayyana zarge-zargen a matsayin marasa tushe, marasa adalci, kuma wadanda ba su dace da tarihin aikinsa na gwamnati ko bayanan gaskiya ba.
Malami ya jaddada cewa babu wata hukuma ta tsaro, doka ko leken asiri, a ciki ko wajen Najeriya, da ta taɓa zarginsa, kiran shi domin tambaya, bincikensa, ko gurfanar da shi game da daukar nauyin ta’addanci ko wani laifi makamancin haka.
“Da farko, ina fayyacewa a fili cewa ban taɓa samun zargi, gayyata, bincike ko gurfanarwa ba daga kowace hukuma ta tsaro, doka, ko leken asiri ciki ko wajen Najeriya dangane da daukar nauyin ta’addanci ko makamancin haka.”

Kara karanta wannan
Majalisa ta gaji da jira, ta taso Tinubu a gaba kan masu ɗaukar nauyin ta'addanci
"Na biyu, tsohon jami’in sojan da aka ambata a matsayin tushen labarin ya bayyana a sarari cewa bai zarge ni ko waɗanda aka ambata da taimaka wa ta’addanci ba.”
- Abubakar Malami

Source: Facebook
Malami ya bayyana cewa bayanin tsohon sojan ya takaita ne kawai ga ikirarin cewa wasu da ake zargi suna da wani nau’i na “hulɗar kasuwanci” ko “alaƙar aiki” da wadannan mutanen.
“Wannan muhimmin bayani an boye shi ta hanyar yadda aka gabatar da labarin, wanda zai iya karkatar da hankalin jama’a su yanke hukunci marar tushe da zai iya cutar da ni."
"Abokan hamayyar siyasa sun yi amfani da shi wajen kirkiro mummunar fahimta da yaudara ta siyasa, suna nufin nuna kamar ina da hannu a daukar nauyin ta’addanci."
- Abubakar Malami
Abubakar Malami ya amsa gayyatar EFCC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami, ya amsa gayyatar da hukumar EFCC ta yi masa.
Tsohon Ministan ya bayyana cewa an sake shi bayan ya amsa tambayoyi yayin da ya kai kansa gaban hukumar yaki da cin hancin.
Malami ya bayyana cewa ganawarsa da hukumar yaƙi da cin hancin ta kasance cikin nasara, inda ya kara da cewa an sa masa wani sabon lokaci domin ci gaba da tattaunawa da masu bincike.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
