To Fa: An Kama Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa Ta Kano, Muhuyi Magaji
- Dakarun 'yan sanda daga Abuja sun kama tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano (PCACC), Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado
- Rahoto ya nuna cewa jami'an tsaron sun dura ofishinsa da ke titin Zaria a cikin birnin Kano cikin shirin ko ta kwana, daga bisani suka tafi da shi
- Shaidu sun ce Rimin Gado ya nemi a nuna masa takardar izinin kamu amma yan sandan suka fada masa suna bin umarni ne daga Abuja
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - 'Yan sanda sun kama tsohon shugaban Hukumar Karɓar Korafe-Korafe da Yaki da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC), Muhuyi Magaji Rimin Gado.
Rahoto ya nuna cewa Muhuyi ya shiga hannun ‘yan sanda ne bayan wasu jami'ai dauke da manyan makamai sun mamaye ofishinsa na aikin lauya da ke Kano, ranar Juma’a.

Source: Facebook
Yadda aka kama Muhuyi Rimin Gado a Kano
Ganau sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa wata mota dauke da dakaru na musamman cikin shirin ko ta kwana ce ta tsaya a kofar ofishin nasa da ke kan titin Zaria Road.
Jami'an tsaron sun umarci jama’a da kada su kusanci wurin, tare da barazanar bude wuta ga duk wanda ya kuskura ya tsoma baki.
Rimin Gado, wanda aka yi awon gaba da shi nan take, ya nemi jami'an tsaron su nuna masa takardar izinin kama shi ko a sanar da shi dalilin tsare shi.
Sai dai dakarun ba su nuna masa takarda ba, amma sun jaddada masa cewa suna bin umarni ne daga Hedikwatar ‘Yan Sanda ta Abuja.
Lauya Ridwan Zakariyya, wanda ya shaida lamarin, ya ce daga baya sun tafi da Rimin Gado zuqa Hedikwatar ‘Yan sanda ta jihar Kano da ke Bompai.
Ya kara da cewa jami’an sun bayyana kansu da dakarun sufetan yan sanda na musamman, IGP Squad daga Abuja, kuma sun yi yunkurin kwace wayarsa tare da yi masa barazanar harbi.
Ba wannan ne karo na farko ba
Wannan shi ne karo na biyu a cikin shekarar 2025 da jami'an tsaro ke kamawa tare da tsare Rimin Gado, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
A farkon watan Janairu, dakarun sashin IGP Monitoring Unit sun kama shi kan batun kwace wani gida da ake zargin mallakar babban jigon jam’iyyar APC ne. Sai dai daga baya an sake shi.

Source: Twitter
Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kano, CSP Abdullahi Kiyawa, ya ci tura, domin bai dauki kiran waya ba kuma bai turo amsad tes da aka tura masa ba har zuwa lokacin hada rahoton nan.
Gwamna Abba ya nada magajin Rimin Gado
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada Saidu Yahya a matsayin sabon ahugaban hukumar PCACC ta jihar Kano.
Hakan na zuwa ne bayan Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ya sauka daga shugabancin hukumar PCACC ta Kano sakamakon karewar wa'adinsa.
Gwamna ya yaba wa tsohon Shugaban Hukumar, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, bisa jajircewarsa, dauriya, sadaukarwa da hidimar da ya yi wa Jihar Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


