'Yan Ta'adda Sun Yankawa Manoman Zamfara Harajin Girbi
- Al’ummomin karkara a Bungudu sun ce ’yan bindiga suna tilasta wa manoma biyan haraji mai tsauri kafin su girbe amfanin gona
- Rahotanni sun nuna cewa Durkai, Honkarhe, Makwa da Kiluta suna daga cikin waɗanda ƴan ta'adda suka umarta da su biya miliyoyin Naira
- 'Yan bindigan suna ci gaba da jefa rayuwar jama'a a cikin rashin tabbas, sannan suna kara tsoratar da jama'a da barazanar hari
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara – Al’ummomin karkara da ke cikin Karamar Hukumar Bungudu a Jihar Zamfara sun sake tashi da wata sabuwar matsala saboda ƴan ta'adda.
Rahotanni sun iske jama'a na cewa nuna ’yan bindiga sun ƙara matsa lamba tare da kakaba haraji mai nauyi kan manoma da ke son girbe amfanin bana.

Source: Twitter
Mai sharhi a kan harkokin tsaro a yankin Arewa maso Yamma, Bakatsine, ne ya wallafa hakan a shafinsa na X a ranar Juma’a.
Ƴan ta'adda sun sako Zamfarawa a gaba
Rahoton ya ce wadanda abin ya shafa sun ce a yanzu ba a bari manoma su kusanci gonakinsu sai sun biya kudin da ’yan bindigan suka ce dole sai an biya.
Al’ummomin Durkai, Honkarhe, Makwa da Kiluta ne suka fi fuskantar wannan matsin lamba, inda ake zargin cewa sun ɗorawa kowane yanki kuɗin da ya zarta ƙarfin jama’ar da ke zaune a can.
Wani mazaunin yankin ya shaida cewa,:
"Manoma a Durkai, Honkarhe, Makwa da Kiluta since an ɗora masu harajin girbi mai nauyi kafin su ciro amfanin gonakinsu."
Harajin da ƴan ta'adda suka dora a Zamfara
Ƴan ta'adda sun dora wa kowane manomi a Durkai da Honkarhe harajin girbi da ya kai N5m.
Makwa kuwa an ce an umurce su da su biya wani adadi mai kauri, yayin da Kiluta ma ta sami irin wannan harajin na N5m.

Source: Twitter
Wadannan buƙatu sun saka jama’ar yankunan cikin fargaba da tashin hankali, musamman ganin cewa manoma su ne ginshiƙan tattalin arzikin yankin.
Rahotannin sun ƙara bayyana cewa lamarin ya kai wani mataki mai ban tsoro, inda ake zargin ’yan bindigan sun fara sa farashin kayayyaki, musamman babura.
Mutane a yankin sun ce farashin babur ɗin Honda ya kai kusan N1.7m saboda tsoma bakin ’yan ta’addan a kasuwa.
Ƴan jarida sun shiga damuwa kan tsaro
Kungiyar yan jarida masu kishin zaman lafiya ta Kano KCJF ta bayyana takaici a kan yadda tsaro ya zama abin siyasantar wa a Arewacin Najeriya.
Kungiyar ta bakin Shugabarta Aisha Ahmad ta ce jihohi irinsu Zamfara da ake siyasantar da batun tsaro yana kara dagula al'amura.
Kungiyar ta ce:
"Wannan ya zargi wannan, wancan ya ce kazaa duk yana taimakawa ƴan ta'adda su ci karensu babu babbaka."
"Irin wannan haraji da ƴan ta'adda ke dorawa mutane zai sa jama'a su koma gare su neman mafita ba gwamnati ba."
Ƴan bindiga sun kai hari a Zamfara
A baya, kun ji cewa 'yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Danjibga da ke ƙaramin hukumar Tsafe a Zamfara, bayan takaddama kan madarar Rufaida Yoghurt da ake sayarwa a cikin ƙauyen.
Mazauna ƙauyen sun ce ƴan ta'addan sun je shagon sayar da yoghurt don saya — amma suka dauka ba tare da biyan kudi ba, lamarin da mai shagon ya ce ba zai lamunta ba.
Daga ƙarshe suka bar yoghurt ɗin a waje suka tafi. Bayan ƙasa da sa’a guda, ‘yan bindigar suka dawo da makamai, suka fara harbe-harbe a cikin ƙauyen tare da kashe mutane.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


