Shugaban Karamar Hukumar da Ke Fama da Rashin Tsaro Ya Raba Motoci ga Kansiloli
- Shugaban Karamar Hukuma ya tallafawa al'ummarsa domin tsayawa da ƙafafunsu a Katsina da ke fama da matsalolin tsaro
- Hon. Abdullahi Sani wanda ke jagorantar karamar hukumar Safana shi ya yi wannan abin alheri wanda ya samu yabo daga gwamna
- Safana na daga cikin ƙananan hukumomi da ke fama da matsalolin tsaro a jihar musamman daga yan bindiga
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Safana, Katsina - Shugaban Karamar Hukuma a jihar Katsina ya yi abin a yaba ga al'ummar yankinsa domin dogaro da kansu.
Shugaban karamar hukumar Safana a Jihar, Alhaji Abdullahi Sani, ya tallafawa mutane 1,322 a yankinsa.

Source: Facebook
An raba motoci ga kansiloli a Katsina
Rahoton Punch ya ce Hon. Sani ya kuma raba motoci 10 ga kansiloli a karamar hukumarsa domin morar romon dimokuraɗiyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun bayyana cewa Gwamna Dikko Radda ne ya kaddamar da shirin a Safana cikin wani taron karfafawa al’ummar yankin guiwa.
Radda ya yaba wa shugaban kananan hukumomin, yana kiran shirin “mafi inganci da karfafawa jama’a” cikin jerin yankunan da ya ziyarta.
Ya kuma jinjinawa shugaban Safana saboda nuna jagoranci nagari da ƙoƙarin inganta al'umma yana cewa hakan misali ne na kawo sauyi mai ɗorewa.
Gwamnan ya ce shirin ya tabbatar da yadda ‘yancin kananan hukumomi ke iya kawo ci gaba ga al’umma ta hanyar ayyuka kai tsaye ga talakawa.
Radda ya bayyana cewa shirin ya nuna yunkurin faɗaɗa kasuwanci, ƙarfafa dogaro da kai, da gina karfin tattalin arzikin al’ummomin Safana gaba ɗaya.
Ya ce:
“Wannan shi ne ainihin manufar ‘yancin kananan hukumomi: ci gaban da ke tasowa daga ƙasa yana inganta rayuwar mutane kai tsaye babu tsaiko.”

Source: Original
Gwamna Radda ya yabawa shugaban karamar hukuma
Radda ya kara da cewa shirin Safana shi ne mafi girma da ya gani tun farkon zagayen da yake yi, ya ce hakan na zama abin koyi ga sauran kananan hukumomi.
Gwamnatin jihar ta ce za ta ci gaba da ɗaukar matakan tallafawa matasa, mata da masu rauni ta hanyar ƙarfafa shirye-shiryen karfafawa al’umma a Katsina.
A nasa bangaren, shugaban ƙaramar hukumar ya gode wa gwamna saboda sakin kudaden da suka ba shi damar aiwatar da wannan gagarumin shirin.
Kayan da aka raba sun haɗa da injunan dinki, nika, babura, injin noma, mota ta musamman ga shugaban APC na yankin.
An kuma raba buhunan fulawa, kekuna ga masu nakasa, tallafin kuɗi ga mata, matasa, masu rauni, da shugabannin APC na ƙaramar hukuma da gundumomi.
Radda ya kuma yi rangadi a dukkan kananan hukumomi 34, tare da kai gaisuwa ga Sarkin Safana, Yariman Katsina Alhaji Sada Rufa’i a lokacin ziyarar.
Yan bindiga: Tsohon mataimakin ciyaman ya kubuta
An ji cewa a kwanakin baya 'yan bindiga suka yi awon gaba da tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.
Yan bindigan sun tsare Nasiru Abdullahi Dayi a hannunsu har na tsawon kwanaki 103 kafin ya shaki iskar 'yanci.
Iyalan dan siyasar sun bayyana halin da suka tsinci kansu a ciki a tsawon kwanakin da ya kwashe ba ya tare da su.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

