Yan Bindiga Sun Kutsa Gidan Malamin Addini a Kaduna da Dare, Sun Sace Shi

Yan Bindiga Sun Kutsa Gidan Malamin Addini a Kaduna da Dare, Sun Sace Shi

  • Wasu yan bindiga dauke da muggan makamai sun farmaki gidan wani malami inda suka yi garkuwa da shi a Kaduna
  • Cocin Katolika a birnin Zaria ya tabbatar da sace Fasto Emmanuel Ezema a gidansa da ke cocin St. Peter’s a jihar
  • An ce ‘yan bindigan sun shiga gidan faston ne da misalin ƙarfe 11:30 na dare, suka tafi da shi ba tare da jinkiri ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Zaria, Kaduna - Hankulan al'umma sun tashi matuka bayan harin yan bindiga a gidan malamin addinin Kirista a jihar Kaduna.

‘Yan bindiga sun sace faston Katolika mai suna Emmanuel Ezema, wanda ke hidima a cocin St. Peter’s da ke unguwar Rumi, cikin jihar Kaduna.

Yan bindiga sun sace Fasto a Kaduna
Taswirar jihar Kaduna da ke fama da matsalolin yan bindiga. Hoto: Legit.
Source: Original

Hakan na cikin wata sanarwar da cocin Zaria ya fitar wanda TheCable ta samu a ranar Laraba 3 ga watan Disambar shekarar 2025.

Kara karanta wannan

Kasa ta rikice: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da kusa a APC

Yan bindiga: Matsalar da Kaduna ke fuskanta

Jihar Kaduna na daga cikin jihohin Arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da matsanancin rashin tsaro na yan bindiga.

Ana ci gaba da kiran gwamnatin tarayya da ta yi kokarin kawo karshen hare-haren yan bindiga domin samun zaman lafiya da kare dukiyoyin al'umma.

Wannan na zuwa ne bayan nadin sabon ministan tsaro a Najeriya bayan murabus din Mohammed Badaru Abubakar.

An rantsar da sabon ministan tsaro a Najeriya

An nada Christopher Musa wanda ya rike mukamin hafsan tsaron Najeriya a baya kafin Bola Tinubu ya sauke su a watan Oktoban 2025.

A jiya Alhamis 4 ga watan Disambar shekarar 2025, Christopher Musa ya karbi rantsuwar kama aiki a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun gwabza kazamin fada da ƴan bindiga a Abuja, an samu asarar rayuwa

Tinubu a nada sabon ministan tsaro a Najeriya
Sabon ministan tsaro, Christopher Musa da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Yadda aka sace Fasto a jihar Kaduna

Cocin ya ce an sace Fasto Ezema ne a cikin gidansa da ke cocin, da misalin ƙarfe 11:30 na daren Talata, 2 ga Disambar 2025.

Sanarwar, mai ɗauke da sa hannun shugaban cocin, Isek Augustine, ta ce ta yi matukar shiga tashin hankali kan lamarin, cewar rahoton Reuters.

“Mun yi matuƙar baƙin cikin sanar da cewa an sace Fastonmu, Rabaran Emmanuel Ezema a gidansa da ke cocin St. Peter’s Catholic Church Rumi, a daren Talata 28 ga Disamba, 2025, da misalin 11:30 na dare.”

Cocin ya kuma roƙi dukkan al'umma da su yi addu’a domin a sako shi cikin gaggawa ba tare da wata illa ba.

Sace Faston ya faru ne a lokacin da matsalolin tsaro suka ƙaru a faɗin ƙasar, musamman hare-haren da ake kai wa al’umma da malaman addini.

Kaduna: 'Yan bindiga sun sace manoma

Mun ba ku labarin cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun yi ta'asa a jihar Kaduna bayan sun ritsa da wasu manoma da ke dawowa daga gona.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ministan tsaro, Mohammed Badaru ya yi murabus

Tsagerun 'yan bindigan sun yi awon gaba da manoman wadanda suka fita neman na abinci a karamar hukumar Sanga.

'Dan majalisa mai wakiltar Jema'a/Sanga a majalisar wakilai, Daniel Amos, ya fito ya yi Allah-wadai da harin 'yan bindigan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.