Hadimin Tinubu Ya Yi Martani Mai Zafi kan Kiran Amurka Ta Hana Dokar Shari'a a Najeriya
- An mika wata bukata a gaban gwamnatin Amurka da ke neman a tilastawa Najeriya soke dokar Shari'ar addinin Musulunci
- Hadimin Shugaba Bola Tinubu ya fito ya yi martani kan wannan bukatar inda ya nuna cewa hakan ba abu ba ne mai yiwuwa
- Daniel Bwala ya bayyana cewa Najeriya kasa ce mai cikakken 'yanci kuma Amurka ba ta da hurumin yi mata katsalandan a harkokinta
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mai ba shugaban kasa shawara kan yaɗa manufofi, Daniel Bwala, ya yi watsi da kiraye-kirayen wasu ‘yan majalisar Amurka da suka nemi Najeriya ta soke tsarin Shari’a.
Daniel Bwala ya ce Amurka ba ta da hurumin yin katsalandan a tsarin mulkin wata kasa mai cikakken ‘yancin kai.

Source: Twitter
Hadimin na Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar Arise Tv a ranar Alhamis, 4 ga watan Disamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bwala ya ce Najeriya na da cikakken 'yanci
Bwala ya ce duk wani yunƙuri na wata kasa wajen umartar Najeriya kan yadda za ta tsara kundin tsarin mulkinta, cin mutuncin ‘yancin da kasar nan ke da shi ne.
Lokacin da aka tambaye shi ko gwamnatin Amurka na da ikon matsa wa Najeriya lamba ta soke dokar Shari’a a jihohin Arewa ko ta yi sauyi a kundin tsarin mulki, sai ya kada baki ya ce:
"Ba su da hurumi. Yin hakan yana nufin take hakkkn kasa cikakken cin gashin kanta da ‘yancinta na cikin gida.”
Bwala ya yi nuni da cewa ma har barazanar mamayar soja da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi, ba ta yi daidai da dokokin duniya da tsarin Amurka ba.
"Ko barazanar mamayar soja ba ta yi daidai da tsarin Amurka ba, domin akwai abubuwa uku kacal da za su iya ba da dama ga wata kasa ta mamaye wata: ko an gayyace ta, ko akwai yaƙi a tsakaninsu, ko majalisar dinkin duniya ta ba da umarni.”
- Daniel Bwala
Ya bayyana cewa Shari’a da ake amfani da ita a jihohi 12 na Arewa ba dokar tarayya ba ce, sai dai tsarin dokokin jihohi da kundin tsarin mulki ya amince da su.
“Shari’a ba doka ce ta kasa baki ɗaya ba. Muna da tsarin tarayya, ko da yake tasu ta fi zurfi.”
- Daniel Bwala
An bukaci Amurka ta sa a hana dokar shari'a
A baya-bayan nan, an bukaci wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka su sa gwamnatin Amurka ta matsa wa Najeriya domin ta soke Shari’a da kuma rushe rundunar Hisbah.
Sun yi zargin cewa wasu kungiyoyin tsattsauran ra’ayi na amfani da su wajen cin zarafin Kiristoci.

Source: Twitter
Sai dai Bwala ya jaddada cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ba ya karkashin amincewar kowace kasa.
"Mun bambanta da su a kan wannan magana ta sauya tsarin mulkinmu. Najeriya kasa ce mai cikakken ikon kanta; ba Amurka ta yi mana mulkin mallaka ba, kuma mu ba Venezuela ba ce.”

Kara karanta wannan
Tsohon hafsan tsaro, Janar Irabor ya fadi 'yan siyasa masu rura wutar matsalar tsaro
- Daniel Bwala
Shugaba Tinubu ya sake nada jakadu
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake zabo mutanen da yake son su zama jakadun Najeriya.
Shugaba Bola Tinubu ya mika sunayensu ga majalisar dattawa domin tantancewa da amincewa da nadin da ya yi musu.
Daga cikin sababbin jakadun akwai tsohon ministan harkokin cikin gida kuma tsohon babban hafsan sojojin kasa, Laftanal Janar Abdulrahman Dambazau (mai ritaya).
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

