Tinubu Ya Ci Gaba da Nade Nade, Ya Sake Zabo Jakadun da Za Su Wakilci Najeriya
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kara mika sunayen mutanen da ya zabo domin ba su mukaman jakadun da za su wakilci Najeriya a kasashen waje
- Mai girma Bola Tinubu ya mika sunayen ga majalisar dattawa domin tantancewa da amincewa da su a matsayin jakadu kamar yadda doka ta yi tanadi
- Karin mutanen ba su daga cikin sunayen wasu mutane fiye da 30 da shugaban kasar ya mika majalisar dattawan Najeriya a makon da ya gabata
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya sake zabo mutanen da yake son naɗawa a matsayin Jakadun Najeriya.
Shugaba Tinubu ya nada tsohon hafsan sojojin ruwa kuma tsohon shugaban riko na Rivers, Ibok-Ete Ekwe Ibas, a matsayin jakada mara gogewa a harkar jakadanci.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta ce daga cikin wadanda aka nada har da tsohon hafsan sojojin kasa kuma tsohon ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya nada karin jakadu
Hakazalika, Tinubu ya kuma naɗa wasu manyan mutane a matsayin jakadu marasa gogewa a harkar jakadanci da suka hada da:
- Tsohon Sanata Ita Enang
- Tsohuwar uwar gidan gwamnan jihar Imo, Chioma Ohakim
- Tsohon Ministan cikin gida kuma tsohon shugaban rundunar sojojin kasa, Laftanal Janar Abdulrahman Dambazau (mai ritaya)
Shugaba Tinubu ya turawa majalisa sunaye
Wadannan sunayen na cikin jerin waɗanda shugaban kasa ya aika wa majalisar dattawa domin samun tantancewa da amincewa a matsayin jakadu.
Sunayensu ba su kasance cikin rukuni na farko na jerin sunayen jakadu da fadar shugaban kasa ta saki ba, jaridar Vanguard ta dauko labarin.
An bayyana sababbin naɗe-naɗen da Tinubu ya yi ne a cikin wata wasiƙa da Godswill Akpabio ya karanta a zauren majalisa yayin zaman majalisar dattawa na ranar Alhamis, 4 ga watan Disamban 2025.
Wace bukata Shugaba Tinubu ya nema?
A cikin wasikar, Shugaba Tinubu ya roki ‘yan majalisa da su duba sunayen cikin gaggawa domin ba gwamnati damar cike guraban muhimman muƙaman diflomasiyya.
Daga nan Akpabio ya tura jerin sunayen zuwa kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar dattawa, tare da umarnin cewa a kammala tantancewar kuma a dawo da rahoto cikin mako guda.

Source: Facebook
Tun da farko, shugaban kasa ya naɗa tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri, tsohon Ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, da tsohon shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, a matsayin jakadu.
Nade-naden na jakadu dai na zuwa ne bayan ofisoshin jakadancin Najeriya da ke kasashen waje sun kasance babu jakadu tun bayan hawan Shugaba Tinubu kan madafun iko.
Tinubu ya nada Ministan tsaro
A baya mun kawo muku rahoto cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya zabi mutumin da zai maye gurbin Alhaji Mohammed Badaru Abubakar a matsayin Ministan tsaron Najeriya.
Shugaba Bola Tinubi ya zabi tsohon hafsan hafsoshin tsaro (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya) a matsayin sabon Ministan tsaro.
Mai girma Bola Tinubu ya aika da sunan Janar Christopher Musa ga majalisar dattawa domin tantancewa tare da amincewa da nadin da aka yi masa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

