Bello Matawalle Ya Samu Kariya Ana tsaka da Kiran Tinubu Ya Kore Shi
- Femi Fani-Kayode ya yi tir da abin da ya kira makarkashiya da ake yi wa Karamin Ministan tsaron, Bello Matawalle domin raba shi da kujerarsa
- Ya ce haɗin gwiwar Matawalle da mai ba da shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ta taimaka wajen murƙushe 'yan ta’adda a shekarun baya-bayan nan
- Duk da haka, tsohon ministan na Najeriya ya ce ya kamata gwamnati ta riƙa bayyana irin nasarorin tsaro da ake samu a fili ba tare da ɓoye su ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Tsohon Ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya bayyana damuwarsa kan abin da ya kira ƙoƙarin bata suna da ake yi wa karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, musamman a dandalin sada zumunta.
Ya ce waɗannan maganganu na fitowa ne daga wasu ’yan hamayya da ke ƙoƙarin rage kimar ministan tun bayan hawa kujerarsa.

Source: Facebook
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, Fani-Kayode ya jaddada cewa Matawalle ya nuna jajircewa da biyayya ga shugaba Bola Ahmed Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce tun shigar ministan ofis, an samu ci gaba mai ma’ana a yaƙi da ta’addanci, musamman sakamakon haɗin kai da yake yi da mai ba da shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu.
Haɗin gwiwar Matawalle da Nuhu Ribadu
Punch ta rahoto Fani-Kayode ya bayyana cewa aiki tare tsakanin Matawalle da Ribadu ya kawo babbar nasara a yaki da ta’addanci a kasar nan.
A cewarsa, wannan haɗin kai ya taimaka wajen kashe ’yan ta’adda masu yawa fiye da yadda aka samu a wasu shekaru da suka gabata.
'Dan siyasar shi ne yake rike da sarautar Sadaukin Shinkafi a Zamfara inda Matawalle ya yi gwamna.
Tsohon ministan ya ce wannan cigaba ne da bai kamata a ɓoye shi ba, saboda yana nuna fa’idar sabuwar dabarar da gwamnati ke amfani da ita wajen magance miyagun laifuffuka.
Ya nuna damuwarsa cewa hukumomi ba su cika bayyana irin waɗannan nasarori ba, lamarin da ya ce ya kamata a gyara domin ƙara wa jama’a kwarin gwiwa.
A cewar Femi Fani-Kayode, bayyana irin wadannan bayanai zai nuna cewa rundunonin tsaro na yin aiki tukuru kuma an samu ci gaba da ake gani a kasa.

Source: Facebook
Fani-Kayode ya karfafa gwiwar Bello Matawalle
Tsohon ministan ya bukaci Matawalle da ya ci gaba da mayar da hankali kan aikinsa ba tare da kula da batutuwan da ke ƙoƙarin tunzura shi ba.
Ya bayyana shi a matsayin mutum mai jarumta, jajircewa da kuma halin jajircewa wajen fuskantar duk wani haɗari. Ya ce wannan halayya tasa ce ta sa su kasance abokai na tsawon shekaru 15.
Fani-Kayode ya ce, duk da mahawara da maganganu marasa tushe da ake yadawa, ya kamata ministan ya ci gaba da jajircewa wajen kare ƙasa da tabbatar da zaman lafiya.
Maganar sabon ministan tsaron Najeriya
A wani labarin, mun rahoto muku cewa sabon ministan tsaron Najeriya, Janar Chiristopher Musa (Mai ritaya) ya bayyana cewa ba zai yarda da sulhu da 'yan bindiga ba.
Janar CG Musa ya kara da cewa ba za a rika biyan 'yan ta'adda masu garkuwa kudin fansa ba, saboda suna kara samun damar sayen makamai da kudin.
Rahotanni sun nuna cewa Janar Musa ya bayyana haka ne a zauren majalisar dattawa yayin da Sanatoci ke tantance shi a ranar Laraba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


