Matan da Shugaba Tinubu Ya Zaba don Zama Jakadun Najeriya a Kasashen Waje

Matan da Shugaba Tinubu Ya Zaba don Zama Jakadun Najeriya a Kasashen Waje

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da karin sunayen mutane 32 da yake son nadawa su zama jakadu.

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Shugaba Tinubu ya aika da sunayen mutanen ne ga majalisar dattawa domin tantancewa tare da amincewa da su a matsayin jakadu.

Shugaba Tinubu ya nada jakadu a Najeriya
Fatima Florence Ajimobi, Farfesa Nora Ladi Daduut da Erelu Angela Adebayo Hoto: Ibrahim Akewusola Oyedepo, Laguma Tutu Mutfwang
Source: Facebook

Tinubu ya mika sunayen jakadu ga majalisa

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka sanya a shafin statehouse.gov.ng a ranar Asabar, 29 ga watan Nuwamban 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ya bukaci majalisar ta duba bukatarsa ta amincewa da mutanen domin zama jakadun Najeriya.

Shugaba Tinubu ya zabo mata don zama jakadu

Daga cikin mutane 32 da Shugaba Tinubu ya aikawa majalisar, 10 daga cikinsu sun kasance mata ne da suka fito daga jihohi daban-daban.

Legit Hausa ta yi duba kan jerin matan da Shugaba Tinubu ya zaba don zama jakadu. Ga jerinsu nan kasa:

Kara karanta wannan

Majalisa ta tantance Oke, Are da Dalhatu, abu 1 ya rage su zama jakadun Najeriya

1. Fatima Florence Ajimobi

Fatima Florence Ajimobi ta kasance uwargidan gwamnan jihar Oyo, marigayi Abiola Ajimobi, daga 2011 zuwa 2019.

A matsayin uwargidar gwamna ta mayar da hankali sosai wajen tallafawa mata da yara, musamman ta hanyar ayyukan jin kai da tallafi.

Jaridar Tribune ta ce ta kafa wasu muhimman gidauniyoyi da shirye-shirye kamar:

  • ABC Foundation — domin saukake samun kulawar lafiya ga marasa ƙarfi
  • Ajumose Food Bank — don tallafawa masu buƙata su samu abinci a cikin jihar
  • Samar da cibiyoyin ICT don bai wa mata damar samun ƙwarewa a fasaha, da kuma ba su horo don dogaro da kai

2. Erelu Angela Adebayo

Erelu Angela Adebayo ta kasance uwargidan gwamnan jihar Ekiti daga 1999 zuwa 2003, lokacin da mijinta, Otunba Niyi Adebayo, ke mulki.

Tinubu ya zabi Erelu Angela Adebayo a matsayin jakada
Uwargidan tsohon gwamnan Ekiti, Erelu Angela Adebayo Hoto: Femi Bobade
Source: Facebook

Ta kasance shugabar kamfanin Afriland Properties Plc, kuma ita ce mace ta farko da ta rike kujerar shugabancin WEMABOD Estates Limited.

Erelu ta kafa gidauniyar Erelu Adebayo Foundation (ERAF), wadda ke taimakawa marasa galihu, musamman mata da yara masu rauni.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ci gaba da nade nade, ya sake zabo jakadun da za su wakilci Najeriya

3. Nkechi Linda Ufochukwu

Nkechi Linda Ufochukwu ta kasance gogaggiyar lauya wadda ta fito daga jihar Anambra.

Ta samu kanta cikin mutanen da Shugaba Bola Tinubu ya nada domin zama jakadun Najeriya a kasashen waje.

Wani rahoto a yanar gizo ya nuna Nkechi Linda Ufochukwu ta taba kasancewa Mai bada shawara ga Ministan kimiyya da fasaha a Najeriya.

4. Grace Folashade Bent

Grace Folashade Bent ta kasance tsohuwar sanata mai wakiltar Adamawa ta Kudu a majalisar dattawa a karkashin PDP.

Tsohuwar sanatar ta koma jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya a shekarar 2021.

Hakazalika ta yi aiki da NTA Kaduna tare da zama mai bada shawara kan harkokin siyasa ga tsohon shugaban PDP na kasa, Audu Ogbeh.

5. Enebechi Monica Okwuchukwu

Enebechi Monica Okwuchukwu ta fito daga jihar Anambra a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Ta kasance ma'aikaciya a ma'aikatar harkokin wajen Najeriya inda yanzu haka take aiki a ofishin jakadancin Najeriya da ke Italy.

Kara karanta wannan

An fara sabon takun saka tsakanin gwamna Fubara da yaran Wike a majalisar Rivers

6. Yvonne Ehinosen Odumah

Yvonne Ehinosen Odumah da Shugaba Tinubu ya zaba don zama jakada ta fito daga jihar Edo a yankin Kudu maso Kudu na Najeriya.

Tana da kwarewa a kan harkar ayyukan diflomasiyya inda yanzu haka take aiki a ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar Italy.

7. Nora Ladi Daduut

Farfesa Nora Ladi Daduut ta kasance haifaffiyar karamar hukumar Quan-Pan a jihar Plateau.

Tinubu ya nada Nora Ladi Daduut a matsayin jakada
Tsohuwar Sanata Farfesa Nora Ladi Daduut Hoto: Deejay Demmamaa
Source: Facebook

Ta kafa tarihi ta hanyar zama mace sanata ta farko daga jihar Plateau bayan ta yi nasarar lashe kujerar sanatan Plateau ta Kudu karkashin jam'iyyar APC a shekarar 2020.

8. Mopelola Adeola Ibrahim

Mopelola Adeola Ibrahim na daga cikin jerin sunayen mutanen da shugaban kasa Bola Tinubu ya aikawa majalisar dattawa don tantancewa su zama jakadu.

Ta fito daga jihar Ogun da ke yankin Kudu maso Yamma na Najeriya.

9. Maimuna Ibrahim Besto

Miamuna Ibrahim Besto ta samu kanta cikin jerin sunayen da Shugaba Bola Tinubu ya zaba don nadawa su zama jakadu.

Kara karanta wannan

Mutane masu alaka da zargin EFCC da Tinubu ya naɗa jakadun kasashen waje

Idan majalisa ta amince da nadin da aka yi mata, za ta kasance cikin jakadun da za su wakilci Najeriya a kasashen waje.

10. Lola Akande

Loka Akande ta kasance malama ce kuma haifaffiyar jihar Kwara a yankin Arewa ta Tsakiya, yanzu haka tana da shekaru 60 da haihuwa.

Ta yi aiki a jami'ar Legas (UNILAG) kuma ta taba rike kujerar kwamishina a jihar Legas. Bayan nan ta yi fice wajen rubuta littatafai da Ingilishi.

Shugaba Tinubu ya nada Ministan tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya zabi sabon Ministan tsaro bayan murabus din Mohammed Badaru Abubakar.

Shugaba Tinubu ya zabi Janar Christopber Musa (mai ritaya) a matsayin wanda yake son ya nada a kujerar Ministan tsaro.

Mai girma Tinubu ya mika sunan Janar Christopher Musa ga majalisar dattawa domin tantancewa da amincewa da nadin da aka yi masa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng