Ministan Tsaro, Janar Musa Ya Ware Gwamnoni 6 da Suka Yi Fice a Kokarin Samar da Tsaro
- Sabon Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya) ya sha tambayoyi a gaban Majalisar Dattawa yau Laraba
- Da yake jawabi yayin tantance shi, Musa ya ce dole ne gwamnoni, yankuna da hukumomin tsaro su hada kai wajen murkushe ta'addanci
- Ya yaba wa gwamnonin jihohi shida na Kudu maso Yamma bisa yadda suke aiki tare wajen tabbatar da tsaro a yankinsu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - A yau Laraba, 3 ga watan Disamba, 2025, Majalisar Dattawan Najeriya ta tantance tare da tabbatar da nadin sabon ministan tsaro, Janar Christopher Musa.
A lokacin da ake tantance shi, Janar Musa ya jinjinawa gwamnonin jihohi shida da ke yankin Kudu maso Yammacin Najeriya saboda yadda suka hada kai wajen tabbatar da tsaro.

Source: Facebook
Musa ya ce akwai bukatar sauran yankunan kasar nan su yi koyi da gwamnonin Kudu maso Yamma domin magance barazanar ’yan bindiga da hare-haren ta'addanci, in ji Leadership.

Kara karanta wannan
A karshe, majalisa ta amince da nadin Janar Christopher Musa a matsayin ministan tsaro
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Janar CG Musa ya jinjinawa gwamnoni 6
Ya bayyana cewa yankin Kudu maso Yamma na samun ci gaba a fannin tsaro ne saboda gwamnonin yankin sun amince su yi aiki tare a matsayin tsari na hadin gwiwa.
Sabon Ministan ya yi gargadi cewa Najeriya ba za ta iya cin nasara a yaki da rashin tsaro ba sai da ingantacciyar alaƙar aiki tsakanin jihohi, yankuna da hukumomin tsaro.
Ya ce:
“Dalilin da ya sa Kudu maso Yamma ke da kyakkyawan sakamako a fannin tsaro shi ne saboda sun yarda su yi aiki tare. Shi ya sa dole gwamnatocin jihohi su hada kai, domin biyu ta fu daya.
Dabarar da 'yan bindiga ke amfani da ita
Ya ce ’yan bindiga suna amfani da saukin ketare iyakoki, musamman a Arewa maso Yamma, inda suke tserewa zuwa Jamhuriyar Nijar bayan kai hare-hare a Sokoto da sauran jihohi.
“’Yan bindiga ba sa girmama iyaka, saboda idan ka bi su a cikin Sokoto, sai su tsallaka zuwa Nijar. Kuma da zarar sun shiga can, ba za ka iya taba su ba har sai sun dawo,” in ji shi.
Tsohon Hafsan Hafsoshin Tsaro ya bukaci gwamnati ta karfafa rundunar hadin guiwa ta MNJTF domin kara inganta ayyukanta a yankin Nijar, Mali da Burkina Faso.

Source: Facebook
Ya bayyana wadannan yankuna a matsayin babbar hanya da kungiyoyin ta’addanci da masu laifi ke amfani da ita wajen matsawa zuwa Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Yamma.
Janar Musa ya karkare da cewa Najeriya ba za ta yi nasara a yakin da rashin tsaro ba sai dukkan hukumomin tsaro sun yi aiki a dunkule, kamar yadda Channels tv ta kawo.
Majalisa ta gama tantance Janar Musa
A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dattawa ta amince da nadin tsohon hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa a matsayin sabon ministan tsaro.
Mambobin Majalisar sun shafe akalla awanni biyar suna yi wa Janar Musa tambayoyi, a lokacin da suke tantance shi a zauren Majalisa da ke Abuja ranar Laraba.
Sanatoci sun yi nazari sosai kan tarihin Janar Musa, gogewarsa a fagen soja, da kuma jawabinsa game da matsalolin tsaron da ke barazana ga kasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
