Farin Jinin Matawalle Ya Fadada, ’Yan Kudu Sun Roki Tinubu game da Kujerarsa
- Kungiyar NDYC ta yi magana game da tasirin da Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ke da shi a gwamnatin Bola Tinubu
- Wannan kungiya daga Kudancin Najeria ta roƙi Tinubu ya ƙi amincewa da yunkurin batanci da ake yi wa tsohon gwamnan Zamfara
- Ta ce maganganun suna fitowa ne daga masu tsoron tasirin Matawalle a siyasar Arewa da goyon bayansa ga Shugaban kasa Tinubu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kungiyar Niger Delta Youth Congress (NDYC) ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu ya yi duba ga tasirin Bello Matawalle.
Kungiyar ta bukaci Tinubu da da ya yi watsi da abin da ta kira “kazafi” da ake yi wa karamin ministan tsaro, Dr Mohammed Matawalle.

Source: Facebook
An roki Tinubu game da kujerar Matawalle
A cikin sanarwar da ta fitar, NDYC ta zargi masu suka da cewa suna gudanar da wani “shiri na siyasa” da nufin ɓata sunan Matawalle, cewar Vanguard
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ce ana yin haka saboda tsoron tasirinsa a matsayin babban amintaccen Shugaba Tinubu daga Arewa.
Kungiyar ta ce waɗannan maganganu na nufin raunana gwamnatin kafin zaɓen 2027 inda kuma suka roƙi a ci gaba da riƙe shi a majalisar ministoci.
A cewar NDYC, waɗanda ke jagorantar karairayi na siyasa na ganin Matawalle yana taka muhimmiyar rawa wajen daidaita siyasar Arewa, kuma suna ganin cewa raunana shi na nufin raunana tasirin siyasar shugaban kasa a yankin.
Kungiyar ta ce:
“Masu kitsa waɗannan maganganu sun yi imanin cewa raunana Matawalle shi ne hanya mafi sauri ta raunana shirin Shugaba Tinubu da ke kara karfi a Arewa.
"Sun san cewa Matawalle ginshiƙi ne, mai haɗa kai, kuma ɗaya daga cikin manyan katangar Siyasar Arewa da ke goyon bayan Shugaban Ƙasa.”

Source: Original
Gargadin kungiyar game da Matawalle a gwamnati
Kungiyar ta gargadi cewa zai kasance babban kuskure idan Tinubu ya lamunci matsin lambar da ake yi don a rage wa ministan ƙarfi, tana mai cewa hakan zai ƙarfafa masu guiwa a neman kawo rarrabuwa a cikin gwamnatin.
NDYC ta ce wannan yaƙi da Bello Matawalle ba wai domin kishin kasa ba ne, illa siyasar kishi, hassada da tsoron tasirinsa da ke ƙaruwa.
Ta ƙara da cewa:
“Yanzu ya bayyana cewa masu adawa suna son cire shi ne kawai saboda biyayyarsa ga Shugaban Ƙasa na barazana ga shirin su na 2027.”
Kungiyar ta zargi wasu mutane da ɗaukar nauyin yaɗa bayanan ƙarya da juya lamurra don kara ƙiyayya a tsakanin jama’a.
Ta bayyana Matawalle a matsayin jajirtaccen mai goyon bayan gyaran harkokin tsaro kuma aminin Shugaban Ƙasa, cewar The Guardian.
'Yan Arewa sun roki Tinubu kan Matawalle
A wani labarin, Kungiyar Northern Stakeholders Consultative Initiative, (NSCI) ta yi magana bayan jin jita-jitar cewa za a kori Bello Matawalle.
Kungiyar ta bukaci Bola Tinubu ya ci gaba da rike Matawalle a kujerarsa bayan saukar Mohammed Badaru daga mukaminsa.
Ta ce tsohon gwamnan na Zamfara yana taka muhimmiyar rawa wajen tsare-tsare na tsaro a Arewa tare da samun goyon bayan al’umma.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

