"Ba Trump ba ne": Sanata Yari Ya Gano Mutanen da Za Su Magance Matsalolin Najeriya
- Wasu 'yan Najeriya sun rika kira ga shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya tsoma baki kan harkokin Najeriya
- Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari ya fito ya yi suka kan masu yin wannan kiran ga Donald Trump
- Sanatan ya bayyana cewa shugaban kasar na Amurka ba zai iya magance matsalolin da Najeriya ke fuskanta ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma Sanatan Zamfara ta Yamma, Abdulaziz Yari, ya caccaki masu kiga ga Donald Trump ya tsoma baki a harkokin Najeriya.
Sanata Abdulaziz Yari mai wakiltar Zamfara ta Yamma ya jaddada cewa ‘yan Najeriya ne kaɗai za su iya magance matsalolin kasar.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce Sanata Yari ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin 'One Nigeria Project' da kungiyar tsofaffin shugabannin kananan Hukumomi (NALGON) ta shirya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Sanata Yari ya ce kan matsalolin Najeriya?
Sanata Abdulaziz Yari ya ce babu wata kasa ko shugaba daga waje da zai zo ya warware matsalolin Najeriya, domin nauyin ya rataya ne kan ‘yan Najeriya, musamman manyan ‘yan siyasa.
Ya zargi manyan kasa waɗanda ya kiyasta ba su wuce mutum miliyan biyu ba, da haifar da rarrabuwar kai.
Sanatan ya bayyana cewa za a iya kawar da matsalolin tsaro da sauran kalubale, idan manyan kasa suka zauna tsaf suka yi aiki domin ci gaban kasar nan, jaridar The Punch ta dauko rahoton.
Me Yari ya ce kan Shugaban Amurka Trump?
“Amurka tana kiran kanta kasar Allah, amma Najeriya ma ta fi zama kasar Allah. Idan ‘yan Najeriya za su fifita kasa kamar yadda Amurkawa ke yi, za mu ci nasarar shawo kan matsalolinmu."
“Ku daina kiran Trump. Ba shi da hulda da Najeriya.‘Yan Najeriya ne kaɗai za su iya gyara Najeriya.”
- Sanata Abdulaziz Yari
Sanata Yari ya kuma soki masu ɗauke da fasfo biyu, yana cewa sukan yi maganganu ba tare da tunani ba saboda suna da inda za su koma.
Ya sake nanata bukatar karfafa tsarin kananan hukumomi, yana cewa tun 1986 yake bibiyar harkokinsu, kuma samar musu da isasshen kuɗi zai taimaka wajen inganta tsaro da gudanar da mulki mai kyau.

Source: Facebook
Batun 'yancin kananan hukumomi
A nasa bangaren, tsohon Ministan shari'a, Michael Aondoakaa, ya yi kira da a ba shugabannin kananan hukumomi karin goyon baya domin su iya yakar matsalolin tsaro a yankunansu.
Haka kuma, tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bukaci ‘yan Najeriya su mara wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya, tare da guje wa son rai da rarrabuwar kawuna.
Ya kuma nemi a karfafa haɗin kai tsakanin tsofaffi da sababbin shugabannin kananan hukumomi domin ci gaban kasa.
Amurka ta sanyawa 'yan Najeriya takunkumi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta fara daukar matakin ladabtarwa kan wasu mutanen da ake ganin suna goyon bayan muzgunawa Kiristoci a Najeriya.

Kara karanta wannan
Tsohon hafsan tsaro, Janar Irabor ya fadi 'yan siyasa masu rura wutar matsalar tsaro
Gwamnatin Amurka ta sanya takunkumin hana biza ga duk mutanen da suka jagoranta, suka ba da izini ko suke goyon bayan tauye ’yancin addini a Najeriya.
Daukar wannan matakin dai na zuwa ne bayan majaliar dokokin Amurka ta yi zama kan karuwar hare-hare a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

