CBN Ya Kawo Sabuwar Doka kan Ajiya da Cire Kudi a Najeriya, za Ta Fara Aiki a 2026

CBN Ya Kawo Sabuwar Doka kan Ajiya da Cire Kudi a Najeriya, za Ta Fara Aiki a 2026

  • Bankin CBN ta soke kayyade adadin kuɗin da ake iya ajiyewa a bankuna, tare da sabunta wasu dokoki da suka shafi mu'amalar kuɗi
  • Sabon tsarin ya kara adadin kudin da za a iya cirewa mako daga N100,000 zuwa N500,000 ga mutum ɗaya da Naira miliyan 5 ga kamfanoni
  • Rahotanni sun nuna cewa an yi gyaran ne domin rage wahalar mu'amalar kuɗi, inganta tsaro, da kuma takaita yaduwar kuɗin haram a kasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da sabon sauyi a dokokin da suka shafi harkar kudi, inda ya soke takaita adadin kudin da ake iya ajiye wa a bankuna tare da kuma kara iyakar adadin cire kudi a mako.

CBN ya bayyana cewa an yi wannan gyara ne a kokarin da ake yi na rage tsadar sarrafa kudi a kasar, magance matsalolin tsaro da kuma dakile yaduwar safarar kudi.

Kara karanta wannan

An kama wasu 'yan kasashen waje da suka shigo Najeriya ta'addanci

Bankin Najeriya na CBN
Babban bankin Najeriya, CBN a birnin Abuja. Hoto: Getty Images|CBN
Source: Getty Images

Legit ta gano haka ne a cikin wata sanarwa da bankin ya fitar wacce daraktar sashen dokokin kudi, Dr Rita Sike, ta rattaba wa hannu kamar yadda Imrana Muhammad ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sababbin dokokin CBN za su fara aiki a 2026

Bankin CBN ya sanar da cewa daga 1 ga Janairun, 2026, za a soke takaita adadin kudin da mutum ko kamfani zai iya ajiye wa a banki.

Haka kuma, an kara adadin kudin da za a iya cirewa a mako ga mutum ɗaya zuwa N500,000, sannan N5m ga kamfanoni. Duk wanda ya wuce wadannan adadi zai biya kudi kamar yadda dokar ta tanada.

CBN ya kuma soke tsarin da ya bai wa mutum damar cire N5ms sau daya a wata da kuma N10m ga kamfanoni, wanda a baya ake bukatar samun izini na musamman.

Dokokin CBN da suka shafi ATM da POS

A bangaren ATM kuwa, an ce dokar iyakar cire kudi a rana ba ta sauya ba – N100,000, yayin da tsarin mako guda yake N500,000, wanda ya kunshi dukkan hanyoyin cire kudi ciki har da POS.

Kara karanta wannan

Tsohon hafsan tsaro, Janar Irabor ya fadi 'yan siyasa masu rura wutar matsalar tsaro

CBN ya ce duk wanda ya wuce wannan iyaka cikin masu asusun banki zai biya kashi 3 yayin da kamfanoni kuma za su biya kashi 5.

Wasu na cire kudi a ATM
Wasu matasa na cire kudi a ATM. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Vanguard ta rahoto cewa, za a raba kudin harajin da aka karba ne, inda za a ba da 40% ga CBN sannan 60% ga bankin da aka yi ma'amala da shi.

Haka kuma, an umarci bankuna da su rika saka kudi na dukkan nau’ukan takardu a cikin na'urorin ATM domin ba jama'a damar mu'amala da su.

An bukaci CBN ya kawo sababbin takardun kudi

A wani labarin, mun kawo muku cewa wata cibiya mai gudanar da bincke ta bukaci babban bankin Najeriya ya kawo sababbin takardun kudi.

Cibiyar ta nemi bankin CBN ya kawo takardun N10,000 da N20,000 guda daya domin saukaka hada-hadar kudi ga 'yan Najeriya.

A bayanin da cibiyar ta yi, ta ce babbar takardar kudin Najeriya, N1,000 ba ta wadatar da jama'a su saye abubuwa da dama saboda karyewar darajar Naira.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng