An Barke da Farin Ciki a Gaza yayin da Falasdinawa 54 Suka Daura Aure
- Falastinawa 54 sun ɗaura aure a Gaza cikin gine-ginen da suka rushe, wani yunƙuri na farfaɗo da rayuwa bayan shekaru biyu na kisan kiyashi
- Ma’aurata sun bayyana farin cikinsu duk da cewa yawancin su sun rasa gidaje kuma suna rayuwa a sansanonin ’yan gudun hijira a yanzu
- Rahotanni sun bayyana cewa shagalin ya samu tallafi daga gidauniyar Al Fares Al Shahim, wadda ta ba ma’auratan kuɗi domin fara sabuwar rayuwa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Gaza – A cikin birnin Khan Younis da yake cike da rusassun gine-gine, Falastinawa sun gudanar da wani babban bikin aure da ya haɗa angwaye 54, lamarin da ya ba al’umma ɗan haske a lokacin da ake fama da hare-hare.
Rahotanni sun nuna cewa daurin auren ya wakana ne jim kaɗan bayan shekaru biyu na kisan kiyashi da suka tagayyara rayuwar mutane a Gaza.

Source: Getty Images
TRT ta rahoto cewa Eman Hassan Lawwa da Hikmat Lawwa — dukkan su ’yan shekara 27 — sun ratsa tsakiyar ginin da ya rushe sanye da tufafin gargajiya na Falasdinawa, tare da sauran ma’aurata da aka kawata su iri ɗaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka dauren Falasdinawa 54 a Gaza
Rahoton AP ya nuna cewa auren Falasdinawa na daga cikin manyan al’adun yankin, amma rikicin da ake ciki da hare haren Isra'ila ya durƙusar da shagulgulan da aka saba.
Yanzu da aka tsagaita wuta, Falasdinawa sun fara komawa gudanar da bukukuwansu, kodayake ba su daidai da manyan bukukuwan da aka saba yi da shagali mai tsawo.
Sai dai farin cikin ya gaurayu da damuwa, domin fiye da mutane miliyan biyu na Gaza sun rasa gidajensu. A cewar Hikmat:
“Muna son mu yi farin ciki kamar sauran mutanen duniya. A da ina fatan samun gida, aiki da rayuwa cikin kwanciyar hankali. Yanzu kuma fata na shi ne na samu tantin zama.”
“Rayuwa ta fara dawowa kadan-kadan, amma ba kamar yadda muke fata ba.”
Falasdinawa sun samu tallafin aure a Gaza
Shagalin ya samu goyon baya daga gidauniyar Al Fares Al Shahim, wadda ta shirya taron gaba ɗaya tare da ba ma’aurata ɗan kuɗi da kayayyaki domin su fara rayuwa tare.
Rahotanni sun nuna cewa tallafin ya sa ma'auratan farin ciki, musamman wadanda ke ƙoƙarin tsayawa da kafafunsu a lokaci mai matuƙar wahala.

Source: Getty Images
Auren Falasdinawa na gargajiya yawanci biki ne na rana ɗaya ko fiye, mai cike da raye-raye da liyafar abinci mai yawa, inda dangi da abokai ke halarta cikin tufafi na musamman.
Amma wannan lokacin, yawancin waɗannan al’adu sun takaita saboda matsin rayuwa, rasa gidaje da karancin abinci saboda hare-haren Isra'ila.
An yi wa mutane 200 aure a Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta shirya auren ga mutane 200 tare da samar musu da kayayyakin fara rayuwa.
Bayanan da Legit Hausa ta samu sun bayyana cewa marasa karfi ne suka samu shiga shirin auren da gwamna Dauda Lawal ya jagoranta.
Gwaman jihar Zamfara ya tabbatar da an daura auren duk da yadda jama'a suka rika sukar shirin lura da yadda ake fama da matsalar tsaro a jihar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


