Obasanjo Ya Shirya, Zai Bada Shaida a Kotu game da Badakalar Kwangilar Mambilla

Obasanjo Ya Shirya, Zai Bada Shaida a Kotu game da Badakalar Kwangilar Mambilla

  • Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana shirinsa na zuwa kotu don bayar da shaida kan batun kwangilar Mambilla
  • Obasanjo ya ce a mulkinsa ba a taba amincewa da ba kamfanin Sunrise Power kwangila ba, kuma ya kasance a shirye ya kare matsayar Najeriya
  • Tsohon minista Olu Agunloye na fuskantar tuhuma bakwai kan saba umarnin shugaban kasa, karɓar cin hanci da kuma amfani da takardu na bogi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo zai halarci zaman kotu domin bada shaida a kan batun kwangilar samar da wuta ta Mambilla.

Shaidan hukumar EFCC, Umar Babangida da ya bayyana a gaban Mai Shari’a Jude Onwuegbuzie a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ce Obasanjo ya ba shi tabbacin hakan.

Kara karanta wannan

An gano wanda zai iya maye gurbin Badaru a matsayin ministan tsaro

Obasanjo zai je kotu saboda kwangilar Mambilla
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo Hoto: Obasanjo quotes
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa Umar Babangida ya bayyana haka a lokacin da lauyan tsohon ministan wutar lantarki da karafa, Olu Agunloye, ya yi masa tambayoyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana shari'a da Ministan Olusegun Obasanjo

Vanguard ta wallafa cewa Agunloye na fuskantar tuhuma guda bakwai da suka hada da saba umarnin shugaban kasa, karɓar cin hanci da kuma hada takardun bogi.

A cewar EFCC, a ranar 22 ga Mayu 2003 Agunloye ya amince da kwangila ga Sunrise Power and Transmission Company Limited (SPTCL) domin gina tashar wutar lantarki mai karfin 3,960MW.

Obasanjo ya ce bai bayar da umarnin a bayar da kwangilar Mambilla ba
Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban Najeriya Hoto: Obasanjo quotes
Source: Getty Images

Ana zargin Ministan wancan lokaci ya yi gaban kansa duk da an yi watsi da hakan a zaman Majalisar Zartarwa (FEC) da aka yi a ranar 21 ga Mayu.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta bayyana cewa wannan abu da ya yi ya sabawa sashe na 123 na dokar Penal Code.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun yi magana da murya 1 kan matsalar rashin tsaro

EFCC ta sako Ministan Obasanjo a gaba

Hukumar ta kuma ce tsohon ministan ya rattaba hannu kan wasika da ta nuna wai gwamnatin tarayya ta amince da kwangilar — abin da ake zargi ya yi tare da Leno Adesanya na Sunrise, wanda ya tsere.

An ce sun yi amfani da takardu na bogi domin tilasta wa gwamnatin tarayya shiga kwangilar $6bn, lamarin da a yanzu ya jawo doguwar shari'a da gwamnati.

A yayin tamsa ambayoyi, Babangida ya ce a watan Nuwamba 2023, Obasanjo ya rubuta wa Ministan shari'a na kasa wasiƙa yana bayyana cewa ya shirya ya bayyana a kotu ko a mataki na neman a yi sulhu kan batun.

Ya ce:

“A lokacin ganawar mu da Obasanjo, ya ce ya san an tattauna batun kwangilar, amma babu wata amincewa. Wannan bayanin yana cikin kundin taron majalisar zartarwa ta kasa.”

Obasanjo ya ce a lokacin mulkinsa ba a bai wa Sunrise wata kwangila ba, kuma bai san da wata amincewa da aka yi a Mayu 2003 ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da babban hafsan tsaron Najeriya da ya kora daga aiki

EFCC ta kai tsohon minista kotu

A baya, mun wallafa cewa Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta sake gurfanar da tsohon Ministan Wuta da Karafa, Dr. Olu Agunloye, a gaban babbar kotun birnin tarayya da ke Apo, Abuja.

An gurfanar da shi ne kan sabbin tuhuma bakwai da suka shafi karɓar rashawa, almundahana, da kuma bijire wa umarnin shugaban kasa a wani muhimmin lamari da ya shafi kwangilar tashar wutar lantarki ta Mambilla.

M.K. Hussain, ya shaida wa kotu cewa hukumar ta sabunta takardun tuhuma da ta yi wa Agunloye, tare da neman kotu ta sake karanta masa sabbin zarge-zargen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng