Majalisa Ta Sa Lokacin Kada Kuri'a kan Yi Wa Kundin Tsarin Mulki Garambawul
- Akwai kudurori da dama a gaban majalisar wakilai da ke neman a yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 garambawul
- Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu ya bayyana cewa za a kada kuri'a domin yi wa kundin tsarin mulkin garambawul
- Benjamin Kalu wanda shi ne shugaban kwamitin sake duba kundin tsari mulki, ya nuna cewa sun kammala duk wani aikin da ya kamata su yi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Majalisar wakilai za ta kada kuri'a kan yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya garambawul.
Majalisar wakilan za ta kada kuri’a kan muhimman abubuwan da ake son sauya wa a ci gaba da yunkurin yi wa kundin tsarin mulki na 1999 garambawul a ranakun 10 da 11 ga Disamban 2025.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Okezie Kalu, ya sanar da hakan a zaman majalisar na ranar Talata, 2 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan
Tsohon hafsan tsaro, Janar Irabor ya fadi 'yan siyasa masu rura wutar matsalar tsaro
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Benjamin Kalu, wanda shi ne shugaban kwamitin sake duba kundin tsarin mulki, ya ce tattaunawa kan kudurin sauye-sauyen za ta gudana ne a Laraba da Alhamis na wannan makon.
Majalisa za ta kada kuri'ar yin garambawul
Mataimakin shugaban majalisar wakilan ya ce za a gudanar da tattaunawar ne kafin a gudanar da kada kuri’ar mako mai zuwa.
Ya bayyana cewa kwamitin ya kammala dukkan ayyukan da ake buƙata, kuma ana shirya takardun da aka haɗa gaba ɗaya domin gabatarwa ga ’yan majalisa su yi nazari.
A halin yanzu, akwai kudurori 87 da ke son yi wa kundin mulki garambawul, waɗanda suka shafi:
- Gyaran tsarin zaɓe
- Sauye-sauye a bangaren shari’a
- Kafa ’yan sandan jihohi
- Sauye-sauye a harkar kuɗi da rarraba ikon gwamnati
A cikin su akwai kudurorin da ke neman kara kujeru na musamman ga mata, kafa sababbin jihohi da kananan hukumomi, kafa ’yan sandan jihohi da ba kananan hukumomi cikakken 'yancin cin gashin kai.

Source: Facebook
Me ake bukata kafin sauya kundin tsarin mulki?
The Cable ta ce sashe na 9(2) da 9(3) na kundin tsarin mulki na shekarar 1999 na buƙatar a samu amincewar majalisun dokoki na jihohi akalla biyu bisa uku — wato jihohi 24, kafin a iya amincewa da duk wani kudurin sauya kundin tsarin mulki.
A ’yan shekarun nan, ana ta ƙara samun matsin lamba a yi wa kundin tsarin mulki gyara domin a sake fasalin Najeriya, wato a rage wa gwamnatin tarayya iko tare da mika wasu manyan iko zuwa gwamnatin jihohi da kananan hukumomi.
Sauye-sauyen kundin tsarin mulki na karshe ya gudana ne a shekarar 2023, inda tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan kudirori 16 daga cikin waɗanda majalisar ta amince da su, a ranar 17 ga Maris.
Majalisa ta bukaci a dawo da Jonathan gida
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar wakilan Najeriya ta yi magana bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Guinea-Bissau ya ritsa da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya sa labule da babban hafsan tsaron Najeriya da ya kora daga aiki
Majalisar wakilan ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta amfani da diflomasiyya da duk wasu matakai domin tabbatar da dawo da tsohon Shugaba Jonathan daga Guinea-Bissau.
Hakazalika, majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta kara himma wajen kokarin diflomasiyya don sauwaka dawowar Jonathan da kuma fifita tsaron dukkan 'yan Najeriya da rikicin ya shafa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
