An Zo Wajen: Peter Obi Ya Yi Wa Tinubu Raga Raga kan Jakadun da Ya Nada
- 'Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi, ya bi sahun mutanen da ke magana kan jakadun da Shugaba Bola Tinubu ya nada
- Peter Obi ya nuna takaicinsa kan wasu daga cikin sunayen mutanen da ake so za su wakilci Najeriya a kasashen waje
- Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana cewa akwai wadanda ko kadan bai kamata su zama wakilan Najeriya ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya yi magana kan jakadun da Shugaba Bola Tinubu ya nada.
Peter Obi ya ce wasu daga cikin sunayen da Shugaba Tinubu ya aika wa majalisar dattawa domin tantancewa a matsayin jakadu sun “bashi mamaki.”

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wani rubutu da tsohon gwamnan na jihar Anambra ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya sa labule da babban hafsan tsaron Najeriya da ya kora daga aiki
Me Peter Obi ya ce kan jakadun Tinubu?
Peter Obi ya bayyana takaicinsa kan jerin sunayen, yana mai cewa akwai wasu sunaye da ba su dace ba.
“Eh, wasu daga cikin sunayen da ake yadawa a matsayin waɗanda za su wakilce mu a matsayin jakadu sun ba ni mamaki."
"Amma da irin shugabancin da ya bari sakaci, rashawa da rashin hukunta masu laifi ya zama al’ada, wa kuma kuke tsammanin za su zaɓa?”
- Peter Obi
Peter Obi ya koka wuyar da ake sha
Tsohon gwamnan na Anambra ya kuma yi tsokaci kan wahalhalun tattalin arziki da ke addabar miliyoyin iyalai a cikin ƙasa.
“Lokacin da ake kashe mutanenmu, shugabanninmu suna ta shirya liyafa. An hana yara zuwa makarantu, amma ’yan siyasa suna rawa suna murna.”
“Lokacin da iyalai suka kasa samun abin da za su ci, waɗanda ke mulki suna tarbar masu sauya sheƙa suna musayar kyaututtuka, kamar babu abin da ke faruwa, alhali Nigeria tana ƙonewa.”

Kara karanta wannan
Nuhu Ribadu ya gana da wakilan CAN da iyayen daliban Neja, an ji abin da suka tattauna
“Wannan ba mulki ba ne. Ba jagoranci ba ne. Kuma ba ita ce Najeriya da muka cancanci samu ba.”
- Peter Obi

Source: Facebook
Nada jakadun Tinubu ya jawo cece-kuce
Baya ga Peter Obi, wasu ’yan Najeriya da dama sun nuna damuwa game da sunayen da Tinubu ya gabatar a jerin jakadu.
Tashar Channels tv ta ce tsohon babban sakataren ma’aikatar harkokin kasashen waje, Joe Keshi, ya soki jerin sunayen, yana tambayar nagartar wasu daga cikin waɗanda aka zaɓa.
Ya ce akwai wadanda ko ta wane ma’auni ba su da abin da zai sa su su yi aikin diflomasiyya.
Sai dai Ademola Oshodi, mai ba Shugaba Tinubu shawara kan harkokin kasashen waje, ya kare jerin sunayen, yana mai cewa su ne mafi dacewa da gwamnatin Tinubu.
Oshodi ya ce shugaban kasa na da ikon zaɓar duk wanda yake ganin zai iya aiki da shi domin ci gaban kasa.
PDP ta soki Shugaba Tinubu kan nada jakadu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta yi kakkausar suka kan mutanen da Shugaba Bola Tinubu yake so ya nada a matsayin jakadu.
Jam'iyyyar PDP mai adawa ta bayyana cewa ko kadan bai dace wasu daga cikin sunayen su kasance mutanen da za su wakilci Najeriya ba.
Ta bukaci Shugaba Tinubu da ya nada mutane masu nagarta wadanda za su kare martabar Najeriya a idon duniya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
