"Ba Na Addini Ba ne": Zulum Ya Fadi Manufar Rikicin Boko Haram
- Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi tsokaci kan rikicin Boko Haram da ya ki ci ya ki cinyewa
- Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce rikicin ba na addini ba ne kamar yada wasu ke kokarin nuna hakan ga duniya
- Gwamnan ya bukaci Musulmi da Kirista da su hada kai wuri guda domin samo mafita kan rikicin wanda ya jawo asarar rayukan mutane masu yawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi magana kan rikicin Boko Haram da aka dade ana fama da shi.
Gwamna Zulum ya ce rikicin Boko Haram ba rikicin addini ba ne kamar yadda wasu ke kokarin nunawa.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce Gwamna Babagana Zulum ya faɗi haka ne a ranar Litinin yayin da yake tattaunawa da shugabannin Musulmi da Kirista a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Zulum ya ce kan rikicin Boko Haram?
Gwamna Zulum ya yi kira da a rungumi sulhu da zaman lafiya a tsakanin al’ummomin jihar kamar yadda rahoton ya zo a Daily Post.
“Rikicin Boko Haram ba rikicin addini ba ne. Hari ne kan ɗabi’unmu, ɗan Adam da duk abin da muke dauka da daraja, Musulmi ko Kirista.”
“Yana da matukar muhimmanci mu kawar da duk wasu labarai marasa tushe da ke son nuna matsalar tsaronmu a matsayin rikicin addini. Rikicin addini ba halinmu ba ne.”
- Gwamna Babagana Umara Zulum
Zulum: Rikicin ya shafi Musulmi da Kirista
Gwamnan ya bayyana cewa wadanda ke aikata ta’addanci sun kashe Musulmi da Kirista ba bambanci, sun lalata masallatai da coci-coci da irin mummunan zalunci iri ɗaya.
Ya kara da cewa alkaluman mutanen da rikicin ya shafa sun nuna gaskiya mai daci kan abubuwan da ke faruwa.
“Ko da rayuwa ɗaya kacal aka rasa abu ne mai nauyi, gaba ɗaya alkaluma sun nuna cewa mafi rinjayen wadanda suka rasa rayuka, aka sace ko suka tagayyara Musulmi ne.”

Kara karanta wannan
"Mutane suna da mantuwa," Sheikh Gumi ya yi magana kan zargin goyon bayan 'yan bindiga
- Gwamna Babagana Umara Zulum
Zulum ya ce ya kamata wannan bala’i ya haɗa mutanen Borno wuri ɗaya a cikin jimami da karfafa jajircewa domin samar da mafita ta haɗin kai.
Gwamnan ya ce shirye-shiryen gwamnati na sake ginawa, komawa gida da farfadowa suna bisa adalci, gaskiya da rashin nuna bambanci.

Source: Facebook
Wane kokari Gwamna Zulum ke yi?
Zulum ya bayyana cewa gwamnatinsa ta sake gina cibiyoyin ibadar Kirista 45 da Boko Haram ta lalata.
“Wannan ya haɗa da 16 daga Hawul, 11 daga Gwoza, 10 daga Askira-Uba da 8 daga Chibok."
“Ba mu yi hakan don mu nuna alfarma muka yi ba; nauyi ne a kanmu. Kamar yadda muka gina masallatai, kasuwanni, makarantu da gidaje marasa adadi.”
- Gwamna Babagana Umara Zulum
Ya yi kira ga shugabannin addini da su ci gaba da jagorantar zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista, su guji tashin hankali kuma su karfafa sulhu a cikin al’umma.
Gwamna Zulum ya kara da cewa manufar kiran taron ita ce tattauna wani ginshiki na zaman tare wanda zai duba makomar zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kiristoci a jihar.
Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile wani harin 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.
'Yan ta'addan dai sama da guda 300 sun yi yunkurin kai harin ta'addanci a garin Gwoza amma sun fuskanci turjiya daga wajen sojoji.
Dakarun sojojin sun yi nasarar fatattakar 'yan ta'addan yayin da sojojin sama suka yi musu ruwan wuta da jawo hallaka da dama daga cikinsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

