'Yan Bangan Najeriya Sun Budewa Sojojin Kasar Nijar Wuta, Hedikwatar Tsaro Ta Yi Bayani

'Yan Bangan Najeriya Sun Budewa Sojojin Kasar Nijar Wuta, Hedikwatar Tsaro Ta Yi Bayani

  • Rundunar tsaro ta ƙasa ta yi bayani game da rikicin da ya faru a Mazanya, Jibia da ke jihar Katsina tsakanin ‘yan sa-kai da sojojin kasar Nijar
  • An ce rundunar sojojin Nijar ta shiga yankin ne domin ɗebo ruwa, amma girman tawagar ya haifar da zargin kai harin gaggawa daga ‘yan sa-kai
  • Rahotanni sun ce hukumomin tsaro na Najeriya da Nijar sun tattauna nan take, lamarin kuma ya lafa ba tare da wani sabon tashin hankali ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina – Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta fitar da sanarwa domin fayyace rikicin da ya ɓarke tsakanin ‘yan sa-kai na Najeriya da sojojin Jamhuriyar Nijar a ƙauyen Mazanya, karamar hukumar Jibia, a ranar 29, Nuwamba, 2025.

Kara karanta wannan

Wakilan Trump a Najeriya sun gana da hadimar Tinubu kan rashin tsaro

Lamarin ya faru ne lokacin da tawagar motoci biyar na sojojin Nijar – motoci huɗu masu sulke da wata Toyota Jeep – suka shiga yankin domin ɗibo ruwa, al’ada da ake yi tun da dadewa ba tare da wata matsala ba.

Hafsun tsaron Najeriya, Janar Oluyede
Babban hafsun tsaron Najeriya, Janar Oluyede a wani taro. Hoto: Defence Headquaters
Source: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa tawagar ta tayar da hankalin mutanen yankin, lamarin da ya sa ‘yan sa-kai suka ɗauka wata barazana ce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan banga sun budewa sojojin Nijar wuta

Manjo Janar Michael Onoja ya bayyana cewa shigar sojojin Nijar domin ɗebo ruwa abu ne da aka saba da shi na tsawon shekaru, amma wannan karon girman tawagar ya tsorata jama'a.

A bayanin da ya yi, ya ce wannan ne ya jawo harbin farko daga ‘yan sa-kai, lamarin da ya tayar da hargitsi na ɗan lokaci kafin a gano bakin zaren.

Sojojin Najeriya da kwamandan dakarun Nijar sun yi tattaunawa nan take, inda aka ci gaba da aikin ɗibar ruwan kamar yadda aka saba, sannan tawagar ta koma ɓangaren su cikin kwanciyar hankali.

Kiran da kwamandan sojojin Nijar ya yi

Onoja ya ce kwamandan sojojin Nijar ya yi kira da a rika sakin bayanai kafin daukar matakin da zai iya kai wa ga ketare iyaka, musamman idan tawaga mai yawa ce ko kuma idan akwai manyan hafsoshi.

Kara karanta wannan

Jonathan ya gana da Tinubu, ya fada masa abin da ya faru da shi a Guinea Bissau

Ya bayyana cewa rundunar tsaro ta shirya zaman haɗin gwiwa a ranar 1, Disamba, 2025 domin ƙara ƙarfafa hulɗa da kawar da duk wata matsala nan gaba.

Shugaban kasar Nijar na mulkin soja
Shugaban kasar Nijar, Janar Tchiani. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A bangaren Najeriya kuwa, Onoja ya ce:

“Najeriya da Nijar suna da dogon tarihi na hulɗar al’adu, tattalin arziki da tsaro. Haka kuma ƙasashen biyu na aiki tare wajen yaki da ta’addanci, fataucin kayan haram, shige-da-fice ba bisa ka’ida ba da sauran matsalolin iyakoki.”

Rahoton Arise News ya ce ya ƙara da cewa an ɗauki darasi daga wannan al’amari, kuma an fara aiwatar da matakan gyara domin tabbatar da cewa ba a sake samun irin wannan kuskuren fahimta ba.

Najeriya na samu taimako a yaki da ta'addanci

A wani labarin, mun kawo muku labari Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya ce Najeriya na samun taimako kasashe a yaki da ta'addanci.

Malam Nuhu Ribadu ya lissafo Amurka, Faransa da Birtaniya a cikin wadanda ke tallafawa Najeriya tare da cewa wasu kasashen Turai ma na bayar da gudumawa.

Rahotanni sun nuna cewa Ribadu ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyara jihar Neja bayan 'yan bindiga masu garkuwa sun sace dalibai a wata makaranta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng