'Yan Bindigan da Suka Sace Amarya da Kawayenta Sun Turo Sako a Jihar Sakkwato

'Yan Bindigan da Suka Sace Amarya da Kawayenta Sun Turo Sako a Jihar Sakkwato

  • Awanni 24 bayan sace amarya da kawayenta a Sakkwato, 'yan bindiga sun tuntubi 'yan uwanta a kauyen Chacho da ke karamar hukumar Wurno
  • A ranar Lahadi da ta gabata ne 'yan bindiga suka shiga har cikin gida, suka tafi da amarya da wasu mutane 12 da tsakar dare a jihar
  • Mahaifin amaryar ya tabbatar da cewa masu garkuwar sun tuntube su amma har yanzu ba su nemi kudin fansa ba tukunna

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto, Nigeria - 'Yan bindigan da suka je har gida suka sace amarya da kawayenta a kauyen Chacho, karamar hukumar Wurno a jihar Sakkwato sun tuntubi iyalansu.

Mahaifin amaryar, Malam Umaru Chacho ya tabbatar da cewa masu garkuwan sun kira su ta wayar salula, amma ba su nemi kudin fansa ba.

Jihar Sakkwato.
Taswirar jihar Sakkwato da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Malam Umaru ya shaida wa manema labarai, ciki har da tawagar Channels TV da ta ziyarci kauyen a ranar Litinin, cewa suna cikin tashin hankali.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi musayar wuta da 'yan ta'adda a Kano, an nemi wasu mutane an rasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da masu garkuwa suka nema

Ya ce masu garkuwar sun yi magana da su, amma ba su bayyana bukatar kudin fansa ba tukuna, sai dai sun nemi su yi magana kai tsaye da basaraken yankin.

Ya roƙi hukumomin tsaro da gwamnati da su ceto waɗanda aka yi garkuwa da su a harin na ranar Lahadi kafin lamarin ya ƙara ta’azzara.

Magidancin ya ce mutane 13 aka yi garkuwa da su a harin da aka kai da tsakar dare, ciki har da amarya, kawayenta, ’yan uwansu maza biyu.

Yadda 'yan bindiga suka sace amarya

A cewarsa, maharan sun shiga kauyen ne kusan ƙarfe 12 na dare, suka nufi gidansa kai tsaye a lokacin yana zaune a kofar gida tare da abokansa.

A cewarsa, maharan sun shiga gidan, suka kutsa dakin amarya, suna tambayar inda ita da kawayenta suke. Sai dai har yanzu an gaza tabbatar da ko cinne aka yi wa amaryar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da amarya da sauran 'yan biki a Sokoto

Malam Umar ya ce maharan sun kuma harbi dansa da bindiga a lokacin harin, wanda ya sa ya ji rauni mai muni a kirjinsa, yanzu haka yana kwance a asibiti ana masa magani.

Yan sanda.
Dakarun 'yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: PoliceNG
Source: Twitter

Ya ƙara da cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalai a ranar Lahadi, inda suka nemi su yi magana da dagacin ƙauyen.

A rahoton Daily Trust, mahaifin amaryar ya ce:

"'Yan bindigan sun kira jiya suka ce suna son yin magana da dagacin ƙauyen. Amma mun gaya musu mu ne mutanen da suka dace mu yi magana da su tunda mu ne iyayen yaran da aka sace. Bayan haka, ba su sake kira ba."

'Yan bindiga sun sanya haraji a Sakkwato

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan bindiga sun jefa mutane cikin tashin hankali da fargaba bayan turo wani sako a jihar Sakkwato.

Rahotanni sun nuna cewa yan bindiga sun kakaba harajin Naira miliyan 20 kan mutanne kauyen Makale, sun kuma sanya haraji a wasu kauyuka fiye da 10.

Wani jagoran al’umma, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da cewa irin wannan haraji na tilas ya zama ruwan dare a wasu garuruwa a Sakkwato.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262