Gwamnonin Arewa Sun Hadu don Samo Mafita kan Rashin Tsaro

Gwamnonin Arewa Sun Hadu don Samo Mafita kan Rashin Tsaro

  • Yankin Arewacin Najeriya na ci gaba da fama matsalolin tsaro wadanda ke barazana ga rayuka da dukiyoyin jama'a
  • Gwamnonin Arewa sun hadu a jihar Kaduna domin tattaunawa kan matsalolin rashin tsaron da suka yi wa yankin katutu
  • Taron na zuwa ne yayin da 'yan bindiga ke ci gaba da addabar jama'ar yankin da hare-hare inda suke kashe bayin Allah tare da yin awon gaba da wasu zuwa daji

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Gwamnonin Arewa da sarakunan gargajiya sun shiga taro kan matsalolin da suka addabi yankin.

Gwamnonin Arewa na gudanar da taron ne a fadar gwamnatin jihar Kaduna a ranar Litinin, 1 ga watan Disamban 2025.

Gwamnonin Arewa sun shiga taro a Kaduna
Wasu daga cikin gwamnonin Arewa a wajen taro Hoto: Ismaila Uba Misili
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa taron ya shafi manyan matsalolin tsaro da ke addabar yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin Arewa sun hadu a Kaduna

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bukaci N150m kudin fansar babban Sarki da suka sace

Gwamnonin da ke halartar taron sun haɗa da Uba Sani (Kaduna), Umar Bago (Niger), Inuwa Yahaya (Gombe), Nasir Idris (Kebbi), Ahmadu Fintiri (Adamawa).

Sauran sun hada da Abdullahi Sule (Nasarawa), Umar Namadi (Jigawa), Dauda Lawal (Zamfara), da Mai Mala Buni (Yobe), da sauran su.

Sarakunan gargajiya, ciki har da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, suna daga cikin mahalarta taron na gaggawa da ake yi a Kaduna, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da hakan.

Mece ce manufar taron?

Babban mai taimakawa gwamnan jihar Nasarawa kan harkokin jama'a, Peter Ahemba, ya bayyana manufar taron.

"Manufar taron ita ce a samo matsaya guda da za ta taimaka wajen magance matsalolin tsaro da ke tasiri ga yankin, tare da tattauna hanya mafi dacewa da za a bi.”
“Sakamakon matsalolin tsaro da ke faruwa a wasu jihohin Arewa, gwamnatin jihar Nasarawa ta ɗauki matakan gaggawa ta hanyar shirya taron tsaro na musamman, inda za a yanke muhimman matakai domin hana duk wani yunkurin tabarbarewar tsaro a jihar.”

- Peter Ahemba

Peter Ahemba ya kuma jaddada muhimmancin rawar da ’yan kasa ke takawa.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya gano matsalolin da ke rura wutar rashin tsaro a Arewa

“Alhakin ’yan kasa ne su ba da gudummawa wajen shawo kan barazanar tsaro a jiha da kasa baki daya." Don haka ya zama dole su rika ba hukumomin tsaro muhimman bayanai game da duk wanda ake zargin yana da halayen aikata laifi.”

- Peter Ahemba

Gwamnonin Arewa sun gudanar da taro a Kaduna
Gwamnonin Arewa yayin taron da suka gudanar a Kaduna Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

'Yan bindiga na kai hare-hare a Arewa

A 'yan kwanakin nan, yankin Arewa ya fuskanci karuwar hare-hare a kan makarantun gwamnati, lamarin da ya sa wasu gwamnatocin jihohi rufe makarantu na ɗan lokaci domin kariya.

A makonnin da suka gabata, ’yan bindiga sun farmaki makarantar GGCSS Maga a jihar Kebbi, inda suka yi garkuwa da akalla ’yan mata 24 tare da kashe mataimakin shugaban makarantar.

Bayan wasu 'yan kwanaki, wasu maharan sun sake kai hari a St. Mary’s Catholic Primary and Secondary Schools da ke Papiri a Jihar Niger, inda suka tafi da fiye da dalibai da ma’aikata 300.

'Yan bindiga sun kai hari a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a wasu kauyukan jihar Kano.

'Yan bindigan sun yi awon gaba da akalla mutane 25 tare da raunata wasu mutum biyu a hare-haren da suka kai a wasu kauyuka na karamar hukumar Shanono.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon gwamna ya riga mu gidan gaskiya a Najeriya, an yi jana'iza

Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan bindigan sun kai hare-haren ne cikin dare lokacin da mazauna kauyukan ke kwance a gidajensu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng