Barazanar 'Yan Bindiga: Gwamnatin Jihar Kano Ta Yi Magana kan 'Yan Acaba
- Gwamnatin Kano ta ce ta samu sahihan bayanan yaɗuwar masu acaba a wasu unguwanni duk da hana su da aka dade da yi
- Ta ce jami’an tsaro suna samun cikakken goyon baya wajen ɗaukar matakai a kan matsalar rashin tsaro da ake samu a jihar
- An fara nazarin shawarwarin jama’a kan ƙarin sa ido da tsauraran matakan tsaro a manyan hanyoyin shiga da fita daga jihar Kano
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ta bayyana cewa tana bibiyar korafe-korafen jama’a dangane da ƙara yaɗuwar sana’ar acaba a sassa daban-daban na Kano.
Mutane na korafi game da 'yan acaba ne bayan fara kai hare-hare da aka yi jihar a 'yan kwanakin nan.

Source: Getty Images
Kwamishinan yada labaran jihar, Ibrahim Waiya ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Magana kan 'yan acaba a Kano
Sanarwar ta ce akwai bayanai da suka nuna yadda acaba ke sake bayyana a unguwanni daban-daban a cikin Kano, duk da cewa wannan sana’a na daga cikin abubuwan da aka haramta a jihar.
An kuma samu rahotannin da ke nuna cewa wasu kananan hukumomi da ke iyaka da Kano na fuskantar irin wannan matsala.
Gwamnatin ta jaddada cewa wadannan bayanai sun sanya ta ɗaukar sababbin matakan tsaro domin tabbatar da cewa duk wata barazana ba ta samun gindin zama ba a jihar.
Kwamishinan yada labaran jihar ya ce za a cigaba da daukar matakai musamman a wuraren da ake zargin akwai waɗanda ba a san ko su waye ba.
Matakan tsaro da gwamnati ta ɗauka
A cewar sanarwar da ma’aikatar yaɗa labarai ta fitar, gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa dukkan hukumomin tsaro suna kan aiki, tare da samun cikakken tallafi daga gwamnati.
Sanarwar ta ce:
“Gwamnati za ta cigaba da tallafawa jami'an tsaro domin tabbatar da cewa sun samu nasara a aikinsu.”
Daily Post ta rahoto cewa an ce dukkan rundunonin tsaro a jihar sun fara tsaurara matakan da suka haɗa da saka idanu, sintiri da karfafa aikin bincike a dukkan kananan hukumomi 44.
Ana nazarin shawarwarin jama’a a Kano
Gwamnatin ta bayyana cewa tana yaba wa jama’a bisa shawarwarin da suke bayarwa, musamman game da tsaurara sa ido a manyan hanyoyin shiga da fita daga jihar.
An ce ana bin shawarwarin tare da mayar da su wani ɓangare na babban tsare-tsaren tsaro da ake gina wa jihar.

Source: Facebook
Gwamnatin ta yi kira ga mazauna Kano da su ci gaba da zama cikin nutsuwa, tare da kai rahoton duk wani abin da suka ga yana da yaƙini zai iya zama barazana ga tsaro.
Abba ya yi magana kan tsaron Kano
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Kano ta ce barazanar tsaro da ake magana a kai ba wata babba ba ce a jihar.

Kara karanta wannan
Yadda 'Yan sanda suka saba alkawarin janye jami'ai daga gadin manya amma ba a cikawa
Abba Kabir Yusuf ya ce ana yada jita-jita game da labaran da suke fitowa daga jihar a kan tsaro ko kai hare-hare.
Gwamnan ya bukaci al'umma su kwantar da hankulansu tare da cewa ana lura da kowane yanki na jihar Kano.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

