Trump na Barazanar Kawo Hari Najeriya, 'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane a Amurka
- Yara masu shekaru takwas, tara da 14 sun kasance cikin waɗanda aka kashe a harin da aka kai a Stockton, California a kasar Amurka
- Jami’ai sun ce harin na iya kasancewa da niyya aka shirya shi yayin da wanda ake zargi ya tsere ba tare da an kama shi ba
- Rahotanni sun bayyana cewa an ji wa mutane 11 rauni, kuma hukumomi suna neman shaidu da bidiyo daga wadanda ke wajen
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Rahotanni daga California a Amurka sun tabbatar da kashe mutum huɗu, ciki har da yara uku, a wani hari da aka kai a wani gidan cin abinci a birnin Stockton.
Hukumomi sun ce yaran da suka mutu suna da shekaru takwas, tara da 14, yayin da mutum na huɗu mai shekara 21 ya rasu.

Source: Getty Images
Rahoton BBC ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren Asabar, inda maharan suka jikkata mutane 11.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumomin yankin sun bayyana cewa harin na iya kasancewa da niyya, duk da cewa ba a bayyana cikakkun bayanai kan musabbabin ba har yanzu.
Mataimakin magajin garin Stockton, Jason Lee, ya bayyana takaicin sa kan aukuwar harin, inda ya ce bai kamata a kashe yara ba.
Yadda aka kai hari a Amurka
Hukumomi sun bayyana cewa harin ya auku ne a wani taron da ya gudana a wani gidan cin abinci a Arewacin jihar California.
Wata jami’a, Heather Brent, ta ce lamarin ya girgiza al'umma yayin da ta tabbatar da cewa bincike yana matakin farko kuma babu cikakkun bayanai a yanzu.
Ta ce alamu na farko sun nuna cewa harin na iya kasancewa na niyya, inda jami’ai ke duba dukkan abubuwan da ka iya haifar da harin.

Source: Getty Images
Magajiyar garin birnin, Christina Fugazi, ta ce wannan lamari abin ɓacin rai ne, wanda ya saba da irin haɗin kai da aminci da ake fata a cikin al’umma.
NBC ta rahoto ta ce:
“Ya kamata iyalai su kasance tare a cikin farin ciki, ba su tsaya a asibiti suna addu’ar ceton ’yan uwansu ba.”
Ana cigaba da bincike a Amurka
Hukumomin jihar California sun sanar da cewa FBI, ’yan sandan Stockton da sauran jami’an tsaro suna aiki tare don gano masu hannu a harin.
Hukumar ta nemi jama’a su ba da bayanan gaggawa da za su taimaka wajen kai wa ga kama wanda ake nema.
A wani lamari dabam, ’yan sandan Stockton sun kama mutane biyar bayan samun rahoton cewa akwai mutane masu ɗauke da makamai a wani yankin da ke kusa daga wurin harin.
Sun samu bindigogi guda biyu, amma har yanzu ba a tabbatar ko suna da alaƙa da harin da ya jawo mutuwar yaran ba.
Labarin sojin Amurka ya firgita 'yan ta'adda
A wani rahoton, kun ji cewa an yada wani labari da hukumomi ba su tabbatar ba game da sintirin jirgin leken asirin Amurka a Najeriya.
Masana tsaro sun ce yada labarin ya tayar da hankalin mayakan ISWAP a Borno wanda hakan ya kai ga sun sauya wajen fakewa.
Wani mai sharhi kan lamuran tsaro ya bayyana cewa yada irin labarin yana iya zama barazana ga yaki da ta'addanci a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


