'Yan Ta'adda Sun Fara Gudu bayan Jin Labarin Zuwan Jiragen Sojan Amurka Najeriya

'Yan Ta'adda Sun Fara Gudu bayan Jin Labarin Zuwan Jiragen Sojan Amurka Najeriya

  • Fitar bayanan yunkurin leken asiri da aka ce na Amurka ne a tafkin Chadi ya jefa tsoro a zukatan wasu 'yan ta'adda
  • Wani rahoto ya ce mayakan kungiyar ISWAP sun canza matsuguni bayan bayanan jiragen ISR sun bayyana a yanar gizo
  • Bayan fitar labarin, an yi kira ga jama'a kan cewa fitar da bayanan tsaro irin wadannan na iya jefa sojoji cikin hadari

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno – Fallasar bayanan sirri a kafafen sada zumunta game da ayyukan leken asiri na Amurka a yankin Tafkin Chadi ta janyo cikas ga yaki da ta’addanci.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya tilasta wa wasu mayakan ISWAP sauya matsuguni a yankin.

Wasu jiragen yakin Amurka
Wasu jiragen yaki na sintiri a sama. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Wannan bayani ya fito daga majiyoyi masu sahihanci da suka tattauna da Zagazola Makama game da tasirin matsalar kamar yadda ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kogi ta sha alwashi bayan 'yan bindiga sun tattaro fasto da masu ibada a coci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai har yanzu hukumomin Najeriya ko Amurka ba su fitar da bayani ba domin gaskatawa ko karyata labarin.

'Yan ta'adda sun firgita da jin labarin jiragen Amurka

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa duk da ba a samu yawan mayakan ISWAP a yankin Krinwa kwanan nan ba, fallasar bayanan ISR ta tayar masu da hankali.

An ce wannan ya sa suka sake matsawa daga Dogon Chikun zuwa Bulabulin domin gujewa yiwuwar hare-haren sama a wuraren da aka gano.

Wata majiyar tsaro ta ce:

“Ana wallafa bayanan aikin ISR a kafafen sada zumunta, ’yan ta’adda suka fahimci cewa ana bin diddigin su, sai suka fara sauya waje.
"Irin wannan fallasa na jefa dukkan ayyukan cikin hadari tare da barazana ga lafiyar jami’an tsaro.”

Wata majiyar ta kara da nuna tasirin lamarin a kan hadin gwiwar Najeriya da kasashen waje wajen yaki da ta’addanci. Ta ce:

Kara karanta wannan

An gwabza fada tsakanin sojoji da 'yan Boko Haram sama da 300 a Borno

“Dole mutanen da ke yada bayanan sirri su gane cewa ba duk abin da ake gani ake wallafawa ba. Irin wannan fallasa barna ce. ’Yan ta’adda ma na bibiyar wadannan shafuka.”

Tasirin yada bayanan sirri a yanar gizo

Masana tsaro na cigaba da gargadin cewa fallasa bayanan leken asiri a lokaci-lokaci na iya bai wa kungiyoyin ta’addanci damar kauce wa hare-hare da kuma sake tsara dabarunsu.

A wannan yanayi, fallasar ta tilasta mayakan ISWAP su matsa zuwa sabon wuri, matakin da ke iya tsawaita yaki da tashe-tashen hankula a yankin Tafkin Chadi.

Ana kuma kallon lamarin a matsayin gargadi ga masu wallafa bayanai a shafukan sada zumunta da ke daukar bayanan tsaro a matsayin abin nishadi.

Wani mai sharhi kan lamuran tsaro ne ya wallafa a X cewa jiragen yakin Amurka na sintiri a yankin Arewa maso Gabas domin gano wajen da mayakan ISWAP ke fakewa.

An kara wa wasu sojojin Najeriya matsayi

A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojojin kasan Najeriya ta tabbatar da karin matsayi ga wasu manyan jami'anta.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'ai sama da 20 ne suka zamo Manjo Janar daga Birgediya Janar da suke a baya.

Kara karanta wannan

Malami: EFFC ta gayyaci ministan Buhari kwanaki bayan cewa zai yi takara a 2027

Haka zalika rundunar ta bayyana cewa jami'ai 77 ne aka kara wa matsayi daga Kanal zuwa Birgediya Janar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng