'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Amarya da Sauran 'Yan Biki a Sokoto

'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Amarya da Sauran 'Yan Biki a Sokoto

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun kawo gagarumin cikas a wani shirin daurin aure da ake yi a jihar Sokoto
  • Tsagerun 'yan bindigan sun yi awon gaba da amarya tare da wasu 'yan biki a karamar hukumar Wurno
  • Shugaban jam'iyyar APC na jihar Sokoto ya tabbatar da aukuwar harin amma bai fadi adadin mutanen da 'yan bindiga suka sace ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - 'Yan bindiga a ranar Asabar da daddare sun yi awon gaba da amarya, kawayenta, da wasu baƙi a kauyen Chacho, karamar hukumar Wurno ta jihar Sokoto.

Harin na 'yan bindigan ya katse shirin ɗaurin aure da aka tsara gudanarwa washegari.

'Yan bindiga sun sace mutane a jihar Sokoto
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu da Sufeto Janar na 'yan sanda Hoto: @Ahmedaliyuskt, @PoliceNG
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa maharan sun mamaye kauyen ne kusan karfe 12:00 na dare, inda suka rika harbi a iska kafin su tafi da mutanen.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai hari a Kano, sun yi kisa da sace mutane

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mazauna yankin sun ce matan da suka taru domin taimaka wa amaryar wajen shirye-shiryen aure na daga cikin waɗanda aka sace.

Me hukumomi suka ce kan harin?

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Sokoto, Hon. Isah Sadeeq Achida, ya tabbatar da cewa an sace mutane a kauyen.

Sai dai bai tabbatar ko amaryar na cikin wadanda aka dauka ba, kuma bai iya tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba.

Legit Hausa ta kasa samun mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, DSP Ahmed Rufai, domin bai ɗauki kiran waya ba kuma bai dawo da amsar sakon da aka tura masa ba.

'Yan bindiga na kai hare-hare a Sokoto

Lamarin ya faru ne sa’o’i kaɗan bayan an biya kuɗin fansa na Naira miliyan 4 da babur domin samun 'yancin wasu mutane da aka sace a garin Rabah, abin da ya sake tayar da hankula game da tabarbarewar tsaro a fadin jihar.

Kara karanta wannan

An gwabza fada tsakanin sojoji da 'yan Boko Haram sama da 300 a Borno

Chacho wanda yake nan ne garin da kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Sokoto, Alhaji Shehu Alhaji Chacho, ya fito, ya zama sabon wurin da ’yan bindiga suka kai wa hari cikin jerin hare-haren da suka shafi wasu al’ummomi.

Mazauna yankin sun ce suna cikin tsananin fargaba sakamakon hare-haren da ake ta kaiwa a yankuna makwabta.

Jama'a sun koka kan harin 'yan bindiga

Wani mazaunin kauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana harin da cewa abin takaici ne.

Ya bayyana cewa mata, yara da tsofaffi sun gudu cikin daji domin tsira yayin da ’yan bindigan suka yi ta harkokinsu ba tare da wani kalubale ba.

'Yan bindiga sun sace amarya a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Hakazalika ya kara da cewa har yanzu ’yan bindigan basu tuntubi iyalan amaryar ko shugabannin al’umma ba, lamarin da ya kara dagula hankalin ’yan uwa da ba su san halin da waɗanda aka sace suke ciki ba.

'Yan bindiga sun sace mutane a coci

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai wani harin ta'addanci cikin wani coci a jihar Kogi.

'Yan bindigan sun kai harin ne a Cocin Cherubim da Seraphim da aka kafa a garin Ejiba da ke Karamar Hukumar Yagba ta Yamma.

Kara karanta wannan

Ana murnar ceto daliban Maga, 'yan bindiga sun kashe jami'an hukumar NIS a Kebbi

Mazauna yankin sun bayyana cewa an shiga tashin hankali bayan da maharan dauke da bindigogi suka afka cocin ba tare da wani gargadi ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng