Obasanjo Ya Fadi Yadda Suka Yi da Gumi da Ya Je Wurin Boko Haram a Sambisa

Obasanjo Ya Fadi Yadda Suka Yi da Gumi da Ya Je Wurin Boko Haram a Sambisa

  • Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana abin da Sheikh Ahmad Gumi ya fada masa game da yaran Boko Haram a dajin Sambisa
  • Gumi ya shaida wa Obasanjo cewa mafi yawan yaran ba su kai shekara 15 ba, suna dauke da makamai kuma suna ta'ammali da miyagun kwayoyi
  • Gumi ya na shan suka game da neman shiga tsakanin gwamnati da yan bindiga domin tabbatar da an samu zaman lafiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon shugaban kasa a Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya yi magana game da yaki da Boko Haram a lokacin mulkinsa.

Obasanjo ya bayyana abin da Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya fada masa game da tasirin da Boko Haram ke da shi.

Yadda Gumi ya gargadi Obasanjo game da Boko Haram
Olusegun Obasanjo da Sheikh Ahmad Mahmud Gumi. Hoto: Dr. Ahmad Mahmud Gumi, Anthony Devlin-WPA Pool.
Source: Facebook

Obasanjo ya fadi tasirin Boko Haram a mulkinsa

Kara karanta wannan

Natasha ta yi barazana ga Sanata kan sakon WhatsApp, ta sha alwashin tona asiri

Hakan na cikin wani bidiyo da @ChuksEricE ya wallafa a shafin X a yau Lahadi 30 ga watan Nuwambar 2025 da ake ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, Obasanjo ya ce Malam Gumi ya fada masa wasu abubuwa na tashin hankali game da yaran da ke kungiyar Boko Haram a cikin daji.

Ya ce Gumi ya bayyana yadda shan miyagun kwayoyi suka yi tasiri ga matasan da kuma irin makaman da suke dauke da su da suke ganin babu mai iya galaba kansu.

Boko Haram: Yadda ta kaya tsakanin Obasanjo, Gumi

Daga nan, Gumi ya fadawa Obasanjo gaskiyar halin da matasan ke ciki musamman yadda suka kare mafakar da suke ciki.

"Na gana da Sheikh Gumi a lokacin da nake kan mulki bayan ya kai ziyara wurin ’yan Boko Haram a dajin Sambisa.
"Ya shaida min cewa wasu daga cikin yaran ba su kai shekara 15 ba, suna rike da makamai, kuma miyagun ƙwayoyi suka rinjaye su cikin harkar.
"Suna kuma ikirarin cewa suna kare kansu, ya kuma ce idan wani jami’in tsaro ya ce ya shiga yankin, to ba gaskiya yake faɗa ba."

Kara karanta wannan

'Ni ne mafi girman Kirista a gwamnati': Akpabio ya fadi yadda ya taso a kaskance

Obasanjo ya fadi abin da Gumi ya ce masa kan Boko Haram
Tsohon shugaban kasa a Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo. Hoto: @Oolusegun_obj.
Source: Facebook

Yadda rikicin Boko Haram ya jawo asarar rayuka

Boko Haram dai ta yi kaurin suna ne a lokacin mulkin marigayi Umaru Musa Yar'Adua bayan kashe shugabanta, Mohammed Yusuf.

Jagoran kungiyar ya sha fada a wurin karatuttukansa cewa za su kafa daular Musulunci domin watsi da kundin tsarin mulki na dimukradiyya.

Bayan yan sanda sun hallaka shi ne kungiyar ta dawo da karfinta wanda daga bisani rikicin ya dakule tare da jawo asarar rayuka da dukiyoyin al'umma.

Tun daga wancan lokaci da aka kashe shi watau 2009 ake ta fama da matsalar Boko Haram har zuwa wannan lokaci da muke ciki ta shekarar 2025.

Tsaro: Gumi ya fadi yadda ya taimaki Kaduna

Kun ji cewa malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya ce tsaron Kaduna ya inganta da 90% saboda gwamnati ta dauki shawara.

Ya bayyana cewa ana ganin amfanin hawa teburin tattaunawa da 'yan ta'adda domin a samu matsayar kawo karshen kashe jama'a.

Kara karanta wannan

Jonathan ya gana da Tinubu, ya fada masa abin da ya faru da shi a Guinea Bissau

Malamin ya jaddada cewa ba za a samu zaman lafiya ta hanyar zubar da jini kawai ba, illa ta hanyar hada kai da tattaunawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.