Yan Bindiga Sun Bukaci N150m Kudin Fansar Babban Sarki da Suka Sace
- 'Yan bindigar da suka sace babban Sarki a Kwara sun kira iyalinsa da safe, suna neman miliyoyin kudin fansa kafin su sake shi
- Basaraken ya bace ne a gonarsa, inda aka tsinci babur dinsa kawai, lamarin da ya tayar da hankalin mazauna yankin
- Wani manomi daga wani kauye mai makwabtaka ya shaida cewa ya ga lokacin da ’yan bindigar suka yi awon gaba da Sarkin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin, Kwara - A karshe, bayan dogon jira, yan bindiga da suka sace Sarki a Kwara sun kira iyalansa domin neman kudin fansa.
'Yan bindiga da suka sace Ojibara na Bayagan, Oba Kamilu Salami a karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara, sun tuntubi iyalinsa a yau Lahadi 30 ga watan Nuwambar 2025.

Source: Original
Rahoton Leadership ya ce maharan sun nemi Naira miliyan 150 a matsayin kudin fansarsa kafin su sake shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwara: Yadda yan bindiga suka sace Sarki
An sace Oba Salami ne a gonarsa da misalin karfe 9:30 na safiyar Asabar 29 ga watan Nuwambar 2025 da muke ciki wanda ya jefa al'ummar yankin cikin matsala.
Al’ummar yankin sun tashi cikin tsananin firgici wasu da ake zargin masu garkuwa ne sun sace Sarkin Bayagan, jihar Kwara.
Shaidu sun bayyana cewa sun ga lokacin da ’yan ta'adda dauke da bindigogi suna tilasta wa sarkin hawa babur a gonarsa.
Har yanzu ba a tabbatar da adadin ’yan bindigar da suka kai harin ba, kuma ba su kira iyalan Sarki Kamilu Salami ba.

Source: Facebook
Yan bindiga sun nemi N150m bayan sace basarake
Wani daga cikin iyalan basaraken ya bayyana cewa ’yan bindigar sun kira su da sanyin safiyar Lahadi 30 ga watan Nuwambar 2025 domin gabatar da bukatarsu.
Iyalan sun tabbatar da cewa maharan sun bukaci kudin fansa har Naira miliyan 150 domin sakin basaraken idan aka biya kudin ba tare da matsala ba.
Wasu daga cikin mutanen da ke da kusanci da basaraken sun tabbatar da cewa ’yan bindigar sun dira gonar, suka yi awon gaba da shi ba tare da wata takaddama ba.
Yadda lamarin ya jefa al'umma cikin fargaba
Hankalin jama’a ya fara tashi ne bayan wasu manoma da ke wurin suka gaza ganinsa, sai dai suka ga babur dinsa a ajiye a cikin gonar.
Wannan ya sa aka shiga neman sa a tsakanin mazauna kauyen wata majiyar yankin ya bayyana cewa wani manomi daga wani kauye na makwabtaka ya shaida da idanunsa yadda aka yi garkuwa da Sarkin.
Yan bindiga sun nemi kudin fansa N3bn
An ji cewa ’yan bindiga sun nemi kudin fansa Naira miliyan 100 ga kowane mutum daga cikin masu ibadar da suka sace a cocin CAC, Eruku.
A kalla mutane 30 zuwa 35 aka yi garkuwa da su yayin harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku a wani yanki na jihar Kwara.
Biyo bayan lamarin, matasa sun gudanar da zanga-zanga, yayin da gwamnan jihar ya nemi karin matakan tsaro a yankin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

