Kwana Ya Kare: Tsohon Shugaban APC kuma Sarkin Igbajo Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Kwana Ya Kare: Tsohon Shugaban APC kuma Sarkin Igbajo Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • An tabbatar da rasuwar Sarkin Igbajo na 30 kuma tsohon shugaban APC reshen jihar Osun, Oba Adegboyega Famodun
  • Iyalan gidan sarauta na Gbeleru sun bayyana cewa marigayin ya rasu ranar Juma'a bayan gajeruwar jinya, yana da shekaru 67
  • Oba Famodunya zama Sarki a 2022 lokacin mulkin APC a jihar Osun amma bayan zuwan Gwamna Adeleke, ya fara fuskantar matsala

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun, Nigeria - Tsohon shugaban jam’iyyar APC na Jihar Osun kuma Sarkin Igbajo na 30 a tarihi, Oba Adegboyega Famodun, ya riga mu gidan gaskiya.

Iyalan gidan sarauta na Gbeleru na masarautar Igbajo ne suka tabbatar da rasuwar basaraken a wata sanarwa da suka fitar.

Oba Adegboyega Famodun.
Sarkin Igbajo kuma tsohon shugaban APC a Osun, Oba Adegboyega Famodun Hoto: Adegboyega Famodun
Source: Facebook

Tsohon shugaban APC a Osun ya rasu

Jaridar Punch ta ruwaito cewa iyalan gidan sarautar sun bayyana cewa Famodun ya mutu ne a ranar Jumma'a, 28 ga watan Nuwamba, 2025 bayan gajeruwar jinya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace mai martaba sarki a jihar Kwara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata sanarwa da Prince Adekunle Famodun ya sanya wa hannu a madadin dangin, ta ce marigayin ya rasu yana da shekaru 67, ya bar mata da ’ya’ya.

A cewar dangin, an nada Oba Famodun tare da ba shi sandar mulki a ranar 24 ga Nuwamba 2022 ta hannun tsohon Gwamnan Osun, Adegboyega Oyetola.

Yadda Oba Famodun ya fuskanci rikici

Sai dai bayan Gwamna Ademola Adeleke ya karbi mulkim jihar Osun, ya soke nadin sarautar amma Babbar Kotun Jihar Osun ta maido shi a matsayin Owa na Igbajo a ranar 30 ga Janairu 2025.

Sanarwar ta jaddada cewa a lokacin mulkinsa, Oba Famodun yi aiki tukuru wajen haɗa kan al’ummar Igbajo, tare da inganta zaman lafiya, fahimtar juna da ci gaba,

Ya kuma bar tubalin jagoranci, hikima da jajircewa da za su ci gaba da haskaka wa al’ummar yankin masarautar Igbajo.

A cewar sanarwar:

“Za a tuna da shi saboda halayensa na son zaman lafiya da kwanciyar hankali, hikima, da jajircewa wajen inganta rayuwar al’umma.

Kara karanta wannan

'Ni ne mafi girman Kirista a gwamnati': Akpabio ya fadi yadda ya taso a kaskance

Kafin nada shi ya zama sarki, Famodun ya rike kujerar shugaban jam’iyyar APC na Jihar Osun, cewar rahoton Daily Nigerian.

Rikicin sarautar Igbajo

A 2024, gwamnatin jihar Osun karkashin Gwamna Adeleke ta amince da nadin Prince Ademola Makinde a matsayin sabon Owa na Igbajo domin maye gurbin Famodun.

Amma APC ta jihar ta soki matakin gwamnati, tana mai cewa:

"Har yanzu ana shari’a kan kujerar Owa, don haka bai kamata a nada sabon sarki ba yayin da ake ci gaba da fafatawa a kotu.

An fara takaddama kan kujerar Sarkin Igbajo ne tun a watan Nuwamba 2022, lokacin da gwamnatin PDP ta Gwamna Adeleke ta tsige Gboyega Famodun, wanda Oyetola ya nada kafin saukarsa daga mulki.

An yi jana'izar tsohon gwamna a Delta

A wani rahoton, kun ji cewa an yi jana'izar tsohon gwamnan mulkin soji na Jhar Kudu maso Gabas (wacce yanzu ta kasu zuwa jihohin Kuros Riba da Akwa Ibom), Paul Ufuoma Omu.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Manjo Janar Paul Ufuoma Omu (mai ritaya) ya mutu yana da shekaru 84 da haihuwa.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon gwamna ya riga mu gidan gaskiya a Najeriya, an yi jana'iza

Jana’izar ta samu halartar manyan baki daga rundunar sojin Najeriya, shugabannin siyasa da sarakunan gargajiya ajihar Delta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262