'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari a Kano, Sun Yi Kisa da Sace Mutane
- 'Yan bindiga na ci gaba da addabar wasu yankunan jihar Kano da ke kan iyaka da wasu sauran jihohi makwabta
- Tsagerun 'yan bindigan sun kai harin ta'addanci a wani kauyen Kano da ke makwabtaka da jihar Katsina, inda suka kashe mutum da sace wasu daban
- Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta bayyana kokarin da take yi domin ganin an kubutar da mutanen da aka sace
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - ’Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Kano.
'Yan bindigan sun kashe mutum daya tare da sace wasu mutane uku a garin Yankamaye, cikin karamar hukumar Tsanyawa ta jihar Kano.

Source: Facebook
'Yan bindiga sun kai hari
Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Ghari da Tsanyawa a majalisar wakilai, Hon. Sani Bala Tsanyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Innalillahi Wainna Ilaihir Rajiun. Mu samu rahoto cewa ’yan bindiga sun kai hari a tsohon garin Yankamaye a karamar hukumar Tsanyawa, inda suka kashe mutum daya tare da sace mutane uku.”
- Hon. Sani Bala Tsanyawa
Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne da misalin karfe 11:00 na dare a ranar Asabar, lokacin da mafi yawan mazauna yankin sun riga sun kwanta barci.
Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Legit Hausa.
"Mun samu rahoton harin kuma an tura jami’ai don tabbatar da ceto waɗanda aka sace.”
- SP Abdullahi Haruna Kiyawa
Yankamaye na daga cikin al’ummomin da ke kan iyaka da karamar hukumar Kankia ta jihar Katsina, yankin da ya dade yana fuskantar hare-haren ’yan bindiga da sace-sacen mutane.
'Yan bindiga na kai hare-hare a Kano
Jaridar ta Leadership ta ruwaito cewa wannan harin shi ne na biyu cikin mako guda a karamar hukumar Tsanyawa.
'Yan bindiga sun sace mata 10 a kauyukan Sundu da Biresawa a ranar Talata. A yanzu haka, har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a san inda aka kai wadanda aka sace ba.

Source: Original
Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga
- Ana wata ga wata: 'Yan bindiga sun tare hanya, sun sace matafiya a jihar Kogi
- Mataimakin shugaban karamar hukuma ya tsira bayan kwashe kwana 103 hannun 'yan bindiga
- Obasanjo ya fadi matsayarsa kan tattaunawa da 'yan bindiga, ya ba gwamnati shawara
'Yan bindiga sun sace sarki a Kwara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga yi awon gaba da wani basarake a karamar hukumar Ifeloldun ta jihar Kwara da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya.
Majiyoyi sun bayyana cewa miyagun 'yan bindigan, sun sace mai martaba Ojibara na Bayagan, watau Oba Kamilu Salami, a cikin garin Ifelodun.
Hakazalika, an bayyana cewa sace Alhaji Salami ne da misalin ƙarfe 9:30 na safe a gonarsa lokacin da wasu ’yan bindiga suka yi wa wurin tsinke dauke da bindigogi kirar AK-47.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

