PDP Ta Taso Tinubu a Gaba kan Nada Jakadu, Ta Bayyana Kuskuren da Ya Tafka
- A ranar Asabar, 29 ga watan Nuwamban 2025 shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da karin sunayen mutanen da yake son nadawa jakadu
- Jam'iyyar PDP mai adawa ta fito ta soki jerin sunayen da shugaban kasar ya tura zuwa ga majalisa domin tantancewa
- PDP ta nuna damuwa da takaici kan ganin sunan tsohon shugaban hukumar INEC a cikin jerin sunayen mutanen da za su zama jakadu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta bukaci a janye jerin sunayen jakadu da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika wa majalisar dattawa.
Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa jerin sunayen cike yake da mutanen da suke da halin rashin gaskiya.

Source: Twitter
Mai magana da yawun jam’iyyar PDP na kasa, Kwamared Ini Ememobong, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sanya a shafin X ranar Asabar, 29 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan
Tsohon shugaban INEC ya samu mukami da Tinubu ya nada sababbin jakadun Najeriya 32
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me PDP ta gayawa Tinubu kan nada jakadu?
Jam’iyyar ta kuma bukaci Shugaba Tinubu ya sake aika jerin sunayen ’yan Najeriya masu kyakkyawan tarihin dimokuradiyya da nagartaccen hali, wadanda za su iya wakiltar kasar cikin girmamawa a kasashen waje.
“Wannan jerin sunayen ya kunshi mutane da dama wadanda suka yi kaurin suna wajen yada farfaganda, ’yan siyasa marasa halin kirki, da jami’an gwamnati wadanda ’yan Najeriya da ma al’ummar duniya ke kallon su a matsayin marasa mutunci da suka yi fice wajen aikata abubuwan da ba su dace da dimokuradiyya ba."
"Wannan lamari abin takaici ne kuma abin kunya a tarihin wakilcin diplomasiyyar kasarmu.”
- Ini Ememobong
Ya kara da cewa yawancin ’yan Najeriya sun fusata da jerin sunayen, duk da cewa hakan ba abin mamaki ba ne ganin tarihin wannan gwamnati da irin salon ta.
“Bugu da kari, babu shakka cewa wanda aka zaba yana nuna dabi’a da darajar wanda ya zabe shi. Ta hanyar mika wannan jerin sunayen, shugaban kasa ya nuna cewa wadannan su ne mutanen da ya fi gani sun dace su wakilci Najeriya a kasashen da za a tura su.”

Kara karanta wannan
Obasanjo ya fadi matsayarsa kan tattaunawa da 'yan bindiga, ya ba gwamnati shawara
- Ini Ememobong
PDP ta soki Tinubu kan nada jakadu
Ya ce jinkirin kusan shekaru uku kafin Shugaba Tinubu ya fitar da jerin sunayen ya nuna cewa akwai karancin mutanen kirki a kewaye da shi.
PDP ta ce ta kadu da ganin sunan tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, a cikin jerin sunayen.
Ememobong ya yi zargin cewa nadin Mahmood Yakubu na iya zama hanyar matsawa sabon shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, domin gudanar da zaben da bai dace ba.

Source: Facebook
“Muna tunatar da shugaban kasa da ’yan Najeriya cewa girman da kasa ke samu a idon wasu kasashe na da nasaba da halin shugaban kasar da jakadun da ya tura ba."
"Don haka, tura jakadu masu tabbatacciyar matsala ta siyasa babban rashin adalci ne ga Najeriya, kuma zai jefa kasar cikin matsanancin koma-bayar martabar diplomasiyya.”
"Saboda haka, PDP na bukatar Shugaba Bola Tinubu ya janye jerin sunayen gaba daya, ya sake turo jerin da zai kunshi mutanen da ke da nagartaccen tarihin dimokuradiyya da halin kirki, wadanda za su iya kawo girmamawa ga Najeriya a kasashen da za su wakilta."

Kara karanta wannan
Tinubu ya nada shugaban NIA da ya shiga badakalar $43m lokacin Buhari a matsayin Jakada
- Ini Ememobong.
Jonathan ya gana da Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya gana da Mai girma Bola Tinubu.
Goodluck Jonathan ya gana da Shugaba Tinubu ne yayin wata ziyara ta musamman da ya kai a fadar shugaban kasa.
Tsohon shugaban kasar ya gana da Tinubu ne a ranar Asabar 29 ga watan Nuwambar 2025 domin yi masa bayani kan rikicin siyasar da ta barke a Guinea-Bissau.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng