‘Ni Ne Mafi Girman Kirista a Gwamnati’: Akpabio Ya Fadi Yadda Ya Taso a Kaskance

‘Ni Ne Mafi Girman Kirista a Gwamnati’: Akpabio Ya Fadi Yadda Ya Taso a Kaskance

  • Godswill Akpabio ya yi magana game da albarkar da Ubangiji ya yi masa a rayuwa bayan daga shi zuwa wannan matsayi
  • Ya ce samun mukaminsa har zuwa Shugaban Majalisar Dattawa bai yiwu ba sai da tagomashin Allah
  • Ya bayyana cewa ko karamin gudummawa ga aikin coci na da lada, yana mai sanar da shirin kaddamar da sabon wurin ibada a Majalisar Tarayya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ba al'ummar Kiristoci shawara game da biyayya ga Ubangiji.

Akpabio ya ce nasarar da ya samu a siyasa daga ƙaramin matsayi har zuwa zama ɗan majalisa mafi girma a Najeriya, alheri ne na musamman daga Allah.

Akpabio ya shawarci Kiristoci kan ba addinin gudunmawa
Shugaban majalisar dattawa a zamansu a Abuja. Hoto: The Nigeria Senate.
Source: Facebook

Legit Hausa ta samu bayanin ne daga wata sanarwa da mai taimaka masa kan yada labarai, Jackson Udom, ya fitar a Facebook.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya yi murabus

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akpabio ya shawarci al'umma kan bautar Ubangiji

Akpabio ya faɗi haka ne lokacin da ake bude sabon ofishin Rector na cocin Regina Coeli da ke Uyo, taron da manyan limamai da shugabanni suka halarta.

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya su dage wajen bauta wa Ubangiji ko da a wane matsayi suke inda ya ce yana alfahari kasancewa a Katolika, domin ya ga yadda ikon Allah ya canja rayuwarsa.

Ya jaddada cewa koda mutum ya bayar da gudummawar “kobo 10” wajen aikin coci, wannan aikin ibada ne Allah zai karɓa da hannu biyu-biyu.

Ya kuma bayyana cewa a cikin makonni ƙalilan, za a buɗe sabon wurin ibada a cikin Majalisar Tarayya da ke Abuja.

Ya ce:

“Ni a matsayina na mafi girman Kirista a gwamnati, Allah ya daukaka ni daga kasa zuwa wannan matsayi, Ina cikin dukkan darikun Kiristoci, amma ina farin ciki kuma ina sa’a kasancewa Katolika.

Kara karanta wannan

Natasha ta yi barazana ga Sanata kan sakon WhatsApp, ta sha alwashin tona asiri

“Idan Allah ya iya ɗaga ni daga wanda ba a sani ba zuwa zama Shugaban Majalisar Dattawa, wanda hakan ke nufin na zama mutum na uku mafi girma a ƙasar nan, to zai iya yi mana duka. Ku dai shirya kanku ku tsayar da kanku don karɓar albarkarsa.”
Akpabio ya godewa Ubangiji kan daukakar da ya ba shi
Shugaban majalisar dattawa a Najeriya, Godswill Akpabio. Hoto: Godswill Obot Akpabio.
Source: Facebook

An yabawa Akpabio kan tallafawa Kirista

A taron, Rabaran John Ayah na Uyo ya yaba wa Akpabio da matarsa, Dr Unoma Akpabio, bisa tallafin da suke baiwa cocin, ciki har da karɓar taron manyan malaman coci na ƙasa da suka yi a Ikot Ekpene.

Ya kuma shawarci Godswill Akpabio kada ya saurari masu sukar sa saboda matsayinsa ya sa mutane suke magana.

Wannan jawabin ya zo ne a lokacin da ake ta jita-jita game da yunkurin sauya shugabancin majalisar.

Sai dai jagoran majalisar, Opeyemi Bamidele, ya musanta cewa akwai wani shiri na tsige Akpabio, yana kira da a maida hankali kan zaman lafiya da hadin kai a majalisar.

Akpabio ya damu kan kashe-kashe a Najeriya

Kun ji cewa shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya koka kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.

Godswill Akpabio ya bayyana cewa yana shiga cikin mawuyacin hali idan ya ji rahoton cewa an kashe mutane.

Kara karanta wannan

Martanin Barau da gwamnatin Kano ta nemi a cafke shi saboda zargin ingiza rashin tsaro

Shugaban majalisar ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na bakin kokarinta wajen magance matsalar rashin tsaro.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.