Mataimakin Shugaban Karamar Hukuma Ya Kubuta bayan Kwashe Kwana 103 Hannun 'Yan Bindiga
- A kwanakin baya 'yan bindiga suka yi awon gaba da tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina
- 'Yan bindigan sun tsare Nasiru Abdullahi Dayi a hannunsu har na tsawon kwanaki 103 kafin ya shaki iskar 'yanci
- Iyalansa 'dan siyasar sun bayyana halin da suka tsinci kansu a ciki a tsawon kwanakin da ya kwashe ba ya tare da su
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - 'Yan bindiga sun saki tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina, Nasiru Abdullahi Dayi.
'Yan bindigan sun yi garkuwa da shi ne a garin Dayi, inda ya shafe kwanaki 103 a hannunsu kafin su sake shi.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa an sake shi ne bayan iyalansa sun biya kuɗin fansa da ba a bayyana adadinsu ba ga wadanda suka yi garkuwa da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mataimakin ciyaman ya kubuta
Da aka tuntube shi, wanda aka sace din ya ce zai yi cikakkiyar magana da 'yan jarida a Katsina a kwanaki masu zuwa.
Sai dai ya bayyana godiya mai yawa ga duk wadanda suka yi masa addu’a da kuma wadanda suka tallafa wajen kubutar da shi.
“Ina godiya ga kowa da kowa da ya taimaka, har da kafafen yaɗa labarai, saboda goyon bayan da ba ya gushewa yayin da nake a hannun masu garkuwa. Na yi alkawarin yin hira ta musamman.”
- Nasiru Abdullahi Dayi
Tun bayan da aka sake shi a ranar Talata, Nasiru Abdullahi Dayi yana karbar magani a wani asibiti a Katsina.
Hon. Nasiru Dayi ya sha wahala sosai
Shaidu sun bayyana cewa ya sha wuya domin ya rame kuma yana a gajiye, yayin da abokai, ’yan uwa da masu tausayawa ke tururuwa domin jajanta masa.
Iyalansa sun ce sun shiga cikin mawuyacin hali a duk tsawon lokacin da aka yi garkuwa da shi, inda suke kwana suna tashi cikin damuwa.
Sun roki gwamnati da ta kara daukar matakai don kare al’ummomin karkara daga hare-haren ’yan bindiga da ke ci gaba da faruwa.
Wani na kusa da shi, Hassan Muhammad Tukur, ya bayyana farin cikinsa kan sakin Nasiru Abdullahi Dayi.
“Muna matukar farin ciki cewa yanzu yana shaƙar iskar ’yanci bayan kwana 103 a hannun masu garkuwa da mutane. Muna roƙon Allah ya hana sake aukuwar irin wannan mummunan lamari.”
- Hassan Muhammad Tukur

Source: Original
Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?
An yi kokarin jin tabbataccen bayani daga rundunar ’yan sandan jhar Katsina, amma ba a samu amsa ba.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Sadik Aliyu, bai dauki kiran wayar da Legit Hausa ta yi masa ba kuma bai biyo ba har zuwa lokacin kammala hada wannan rahoton.
An sace iyalan 'yan bindiga a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa mutanen kauyen Runka a jihar Katsina sun kubutar da mutanensu da 'yan bindiga suka sace.
Sun samu nasarar ne ba tare da biyan ko sisin kwabo ba cikin Naira miliyan 26 da 'yan bindigan suka nema a matsayin kudin fansa.
Mutanen kauyen sun shiga daji inda suka dauke iyalan 'yan bindigan wanda hakan ya tilasta musu sakin wadanda suka sace.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


