Shugaban Kasar da Trump ke Son Cafkewa Ya Fito kan Titi, Ya Fada wa Amurka ko Gezau

Shugaban Kasar da Trump ke Son Cafkewa Ya Fito kan Titi, Ya Fada wa Amurka ko Gezau

  • Shugaban Venezuela, Nicolas Maduro, ya wallafa bidiyo yana tuƙa mota a titunan babban birnin kasar duk da barazanar kama shi
  • Amurka ta saka ladan dala miliyan 50 kan kamo Maduro, abin da ya kara tashin hankali a tsakanin Amurka da gwamnatin Venezuela
  • Tun lokacin mulkin Donald Trump na farko da Joe Biden, an kara tsaurara matakan soji a yankin Caribbean da ke karkashin Maduro

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Venezuela – Shugaban Venezuela, Nicolas Maduro, ya wallafa a bidiyonsa yana tuƙa mota a titunan Caracas domin nuna cewa bai jin tsoro ko damuwa game da yawan sojojin Amurka a yankin.

Wannan ya biyo bayan ladan Dala miliyan 50 (₦72.37bn) da gwamnatin Amurka ta sanya za ta ba duk wanda ya kama shi.

Kara karanta wannan

Ngige: Ministan Buhari ya fadawa Obi yadda 'yan ta'adda suka bude masa wuta

Shugaba Maduro da Donald Trump
Shugaban Venuzuela yana yawo a mota da Trump a gefe. Hoto: Getty Images|Al-Jazeera
Source: Getty Images

Tashar Al-Jazeera ce ta wallafa bidiyon shugaba Maduro yana yawo a kan titunan kasarsa yana yawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maduro ya wallafa bidiyon a shafukan sada zumunta, inda yake kokarin kwantar da hankulan magoya bayansa da na duniya baki daya cewa ba ya jin tsoro, duk da ladar da aka sanya a kansa.

Amurka ta sa kudi a kama shugaban kasar

Tun mulkin shugaban Amurka Donald Trump na farko, ake takun saka da shugaban Venezuela, Maduro.

A shekarar 2017, an zargi Maduro da "kawowa dimokuradiyya cikas" kuma an sanya masa takunkumi.

Daga bisani a 2019, BBC ta rahoto cewa Trump ya yarda da jagoran adawa Juan Guaido a matsayin shugaban kasar.

A karshen mulkin Trump na farko, an sanya ladan Dala miliyan 15 kan kama Maduro, sannan aka kara wasu kan manyan jami’an tsaro na Venezuela.

Manufofin bayar da lada ya ci gaba a karkashin mulkin Biden, inda ladan ya kai Dala miliyan 25, kafin Trump ya dawo ofis a karo na biyu ya kara har Dala miliyan 50.

Kara karanta wannan

Sojar Amurka ta rasu bayan harin da dan bindiga ya kai musu, Trump ya fusata

A cewar lauyan Amurka, Pam Bondi, a wata sanarwa a watan Agusta:

“Maduro ba zai tserewa shari’a ba, kuma za a tilasta masa fuskantar sakamakon laifuffukansa marasa kyau.”

Tashin hankali da ake yi a Caribbean

A halin yanzu, Amurka ta kara yawan sojoji a yankin Caribbean, yayin da take kai hare-hare kan jiragen ruwa da ake zargin safarar miyagun kwayoyi daga Venezuela.

Tashin hankali tsakanin yankunan ya kai matakin da ba a taba gani ba cikin shekaru da dama da suka wuce.

Shugaban Amurka, Donald Trump
Donald Trump na wani jawabi a taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Masana sun yi shakku kan tasirin bayar da lada wajen kawo sauyi a gwamnatocin kasar waje, inda suka ce har yanzu ba a tabbatar da cewa wannan hanya tana da tasiri wajen sauya mulki ba.

Sun ce, a Disamban 1989, Amurka ta sanya ladan Dala miliyan 1 kan Manuel Noriega, shugaban soja na Panama, amma an kama shi ne kawai bayan Amurka ta mamaye kasar.

Sojar Amurka ta mutu bayan kai mata hari

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An harbi sojoji a kusa da fadar shugaban Amurka, White House

A wani labarin, kun ji cewa shugaba Donald Trump ya sanar da rasuwar wata sojar kasar da wani dan bindiga ya kai wa hari.

Donald Trump ya yi magana da iyayen sojar mai shekara 20 yana mai cewa za a dauki matakin da ya dace.

Baya ga haka, shugaban ya ce zai hana 'yan wasu kasashe zuwa Amurka saboda suna kawo ci baya ga kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng