Ngige: Ministan Buhari Ya Fadawa Obi Yadda 'Yan Ta'adda Suka Bude Masa Wuta
- Peter Obi ya ziyarci Chris Ngige domin jajanta masa bayan harin da aka kai wa tawagar tsohon ministan a Anambra
- Ngige ya yi bayani dalla-dalla kan yadda maharan cikin kayan soja da ’yan sanda suka bi tawagarsa suka bude wuta
- An kashe wata mata da ke ɗaukar hoton bidiyo lokacin harin, Obi ya ce hakan na nuna yawan zubar da jini a kasar nan
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Anambra - 'Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LPa zaben 2023, Peter Obi, ya bayyana alhini da mamaki kan harin da aka kai wa tsohon ministan kwadago, Sanata Chris Ngige.
Obi ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin ziyararsa gidan Ngige da ke Alor, karamar hukumar Idemili ta Kudu domin jajantawa masa da iyalansa.

Kara karanta wannan
Ngige: An ji halin da ministan Buhari ke ciki bayan 'yan bindiga sun bude wa motarsa wuta

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a Facebook, Obi ya bayyana cewa labarin harin ya firgita shi, sai dai ya gode wa Allah da ya kare rayuwar Ngige.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A nasa ɓangaren, Sanata Chris Ngige ya bada cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru, yana mai cewa motocin rakiyarsa na dawowa daga wasu ayyuka ne aka kai musu hari.
Yadda aka kai wa Chris Ngige hari
Ngige ya ce maharan sun bi tawagar motocinsa da harbi, inda suka kashe wata mata, sannan suka jikkata ɗan sanda mai tsaronsa kafin su kwace bindigarsa da kayan aikinsa.
Vanguard ta rahoto ya kara da cewa maharan sun yi zargin cewa ’yan sandan da ke tsaronsa ya yi wa gwamnatin dabbobi (Nigeria) aiki.
Tsohon ministan ya ce hakan ya dame shi sosai saboda yana nuna yiwuwar maharan sun fito ne domin kwace makamai da kayan jami’an tsaro.
Ngige ya ce ya riga ya sanar da gwamna Chukwuma Soludo game da faruwar al’amarin, wanda ya tabbatar masa cewa za a bi diddigin lamarin domin gano maharan tare da dakile barazanar tsaro
Obi ya ziyarci Ngige bayan kai masa hari
A ƙarshen ziyararsa, Obi ya gode wa Allah da ya kiyaye rayuwar Ngige sannan ya mika ta’aziyyarsa ga iyalin matar da aka kashe.
Ya bukaci mahukunta da su tabbatar da adalci tare da yin aiki tukuru domin hana sake faruwar irin wannan mummunan lamari.
Peter Obi ya yi Allah wadai da kashe matar da aka yi yayin da take daukar bidiyon harin da aka kai wa Ngige hari yana cewa dole a dauki mataki.

Source: Facebook
'Dan siyasar ya kara da cewa harin ya nuna yadda ake bukatar hadin kai a dukkan matakai wajen magance matsalar tsaro.
Shin harin na nufin kashe Ngige?
A cewar tsohon ministan, har yanzu ba a tabbatar ko harin na nufinsa ne kai tsaye ba, sai dai ya bayyana cewa ana iya gane tawagarsa cikin sauki a yankin.
Da yake ƙarin haske, ya ce maharan na iya kasancewa suna farautar duk wata tawaga da ke tafiya ba tare da jami’an tsaro.
A cikin bayaninsa kan matsalar tsaro, Ngige ya sake jaddada ra’ayinsa na cewa batun shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, ya na bukatar bin hanyar siyasa.
Ngige ya yi magana yana mai bayyana damuwa game da lafiyar Kanu da kuma bukatar sake duba batunsa sosai.
Malami: EFCC ta gayyaci ministan Buhari
A wani labarin, kun ji cewa tsohon ministan shari'a a lokacin marigayi Muhammadu Buhari ya samu gayyata daga hukumar EFCC.
Abubakar Malami ya bayyana cewa zai amsa gayyatar ba tare da dar-dar ba saboda ya yi komai a fayyace a lokacinsa.
Sai dai bai bayyana dalilin da ya sanya EFCC tura masa gayyata ba, kuma ita ma hukumar ba ta fadi dalilin gayyatarsa ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

