An Kara wa Sojojin Najeriya 105 Matsayi, An Samu Sababbin Janarori
- Majalisar sojojin kasa ta amince da ɗaukaka mukamin manyan hafsoshi 105 zuwa Manjo Janar da Birgediya Janar
- An karawa wasu Birgediya Janar 28 matsayi zuwa Manjo Janar, sannan aka mayar da Kanal 77 zuwa Brigediya Janar
- Rahoto ya ce hafsoshin da aka karawa matsayi sun fito daga manyan sassa da cibiyoyin sojojin Najeriya daban-daban
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Majalisar sojojin kasa ta amince da karawa wasu manyan hafsoshin sojin Najeriya guda 105 matsayi.
Jami'in hulɗa da jama’a na rundunar sojin kasa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a wata sanarwa da ya fitar.

Source: Twitter
Rundunar sojojin Najerya ta wallafa a Facebook cewa karin matsayi ya hada da mayar da wasu Brigediya Janar zuwa Manjo Janar da kuma wasu Kanal zuwa Birgediya Janar.

Kara karanta wannan
Majalisa ta tsoma baki da Jonathan ya makale a kasar da sojoji suka yi juyin mulki
An ce matakin ya zo ne a wani muhimmin lokaci da rundunar ke ƙara maida hankali kan inganta jagoranci da ƙwarewar hafsoshi domin magance matsalar da ake samu a fagen tsaro.
Sojojin da suka zamo Manjo Janar
Daga cikin Birgediya Janar 28 da aka ɗaga zuwa mukamin Manjo Janar akwai Birgediya Janar O. Adegbe daga Hukumar Leken Asiri ta Tsaro; Birgediya Janar S.M. Uba, Daraktan Bayanan Tsaro.
Bugu da kari akwai Birgediya Janar R.E. Hedima, mukaddashin Shugaban Leken Asiri na Sojin Kasa; da Birgediya Janar R.T. Utsaha, Mataimakin Daraktan Ayyukan Tsaro.
Haka akwai BirgediyaJanar A.M. Umar na; Birgediya Janar S. Sulaiman, Mataimakin Sakataren Sojoji; Birgediya Janar I.O. Bassey na Cibiyar Ayyukan Sojin Kasa da Birgediya Janar C.A. Ekeator.
Sauran sun haɗa da Birgediya Janar S.Y. Yakasai daga Ofishin Kwamandan Rundunar Sojin Kasa; Birgediya Janar W.L. Nzidee daga Sashen Kayayyaki; Brigediya Janar S.A. Emmanuel.
Cikinsu akwai Birgediya Janar S.S. Tilawan, na Operation Hadin Kai; Birgediya Janar M.O. Agi; Birgediya Janar I.M. Abbas, da Birgediya Janar Z.A. Saidu da aka ɗaga darajarsa bayan rasuwarsa.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: Sojojin Najeriya sun kama gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Taraba
Wadanda suka zama Birgediya Janar
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa wani bangare na sanarwar ya fayyace jerin Kanal 77 da suka samu matsayi na Brigediya Janar.
Wadanda aka mayar Birgediya Janar sun fito daga muhimman wurare da suka hada da asibitocin sojoji daban-daban a fadin kasar nan.
Wasu daga cikinsu sun hada da Kanal Y Ibrahim, Kanal NN Gambo, Kanal A Ali, Kanal R Apata, Kanal MK Akpuogwu, Kanal PU, Kanal MT Nagudu da Kanal O Adole.
Sakon shugaban sojojin Najeriya
Shugaban sojojin kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya taya hafsoshin murna, inda ya bukace su da su nuna kyakkyawan jagoranci da zai tabbatar da amincewar da aka nuna gare su.
Ya jaddada cewa ya dace su nuna jajircewa wajen samo sababbin hanyoyi, dabaru da mafita na zamani domin fuskantar ƙalubalen tsaro da ƙasar ke shiga.

Source: Facebook
Ya tunatar da su kan rantsuwar da suka yi na kare iyakokin ƙasa, yana mai cewa dole ne biyayya ga kundin tsarin mulki ta kasance cikakkiya.
Sojoji sun farmaki 'yan ta'adda a Taraba
A wani labarin, mun kawo muku cewa dakarun sojin Najeriya sun kutsa daji sun farmaki 'yan ta'adda a jihar Taraba.
Rahotanni sun nuna cewa an kai wa 'yan ta'addan hari ne a wani yanki na karamar hukumar Donga bayan samun bayanan sirri.
Wata majiya ta ce dakarun Najeriya sun fara musayar wuta da 'yan ta'addan kafin daga bisani sojoji su fi karfin su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
