Ndume zai Barowa Sanatoci Aiki, Ya Nemi Tinubu Ya Janye 'Yan Sanda a Majalisa

Ndume zai Barowa Sanatoci Aiki, Ya Nemi Tinubu Ya Janye 'Yan Sanda a Majalisa

  • Sanata Ali Ndume ya ce ya kamata umarnin janye ’yan sanda daga tsaron manyan mutane ya shafi majalisar kasa
  • Ya bayyana cewa wasu ’yan majalisar tarayya da ministoci suna da ’yan sanda da ke tsaron matansu da ’ya’yansu
  • Ndume ya yi maganar ne bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarni a janye 'yan sanda ga manyan mutane

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa ya dace umarnin shugaba Bola Ahmed Tinubu na janye ’yan sanda daga tsaron manyan mutane ya shafi 'yan majalisa.

Ndume ya ce wasu ’yan majalisa da ministoci suna amfani da ’yan sanda wajen tsaron iyalansu, abin da ya kira rashin dacewa.

Sanata Ali Muhammad Ndume
Ndume yayin da ya ke wani jawabi. Hoto: Ali Muhammad Ndume
Source: Facebook

Sanatan ya yi wannan jawabi ne a lokacin da yake tattaunawa da tashar Channels Television, inda ya ce akwai yawan ’yan sanda fiye da kima a majalisa, duk da umarnin da shugaban ƙasa ya bayar.

Kara karanta wannan

Daga cacar baki, matasa sun caccaka wa babban dan sanda wuka, ya sheka lahira

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

’Yan sanda sun yi yawa a majalisa' — Ndume

The Cable ta rahoto Ndume ya ce tun da aka bayar da umarnin janye jami'ai, ya yi tsammanin cewa yawan ’yan sandan da ke majalisar kasa zai ragu, amma hakan bai faru ba.

Ya ce:

“Na yi tunanin yau ba zan ga ’yan sanda masu yawa a majalisa ba, amma har yanzu cike take.
"Ban san me IGP yake nufi ba. Wasu abokan aikina, hatta matansu, suna da ’yan sanda masu tsaro. Haka ma ’ya’yansu. Wannan ba dai-dai ba ne.”

Ya kara da cewa akwai manyan jami’an gwamnati da ke tafiya da rakiyar ’yan sanda da yawa, har ma ’ya’yansu na zirga-zirga da tawagar jami'an tsaro kamar shugabanni.

'Wani dan majalisa ya tara 'yan sanda"

Ndume ya bada misalin yadda ya ziyarci wani ɗan majalisa ya tarar da ’yan sanda sama da 10 a gidansa.

A cewarsa:

Kara karanta wannan

Abu ya gagara: Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta baci kan matsalar tsaron Najeriya

“Wasu idan ka gan su suna shigowa, ka ja da baya saboda ka yi zaton shugaban ƙasa ne ko mataimakinsa ke wucewa.”

Korafin Ndume ga Tinubu kan 'yan sanda

Sanatan ya kara da cewa idan Abuja ta kasance mai cikakken tsaro, ko shugaba Tinubu ba zai bukaci rakiyar tawaga mai yawa ba.

Ya ce:

“Idan an tsare Abuja sosai, shugaba ma zai iya tuka kansa. Amma idan ka tsare manyan mutane ka bar talakawa, hakan na kara rashin tsaro.”

Sanatan ya jaddada cewa matakan da Shugaba Tinubu ke dauka kan tsaro suna da kyau, amma akwai buƙatar ƙarin aiki domin tabbatar da zaman lafiya ga kowa a kasar.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu yana wani jawabi. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Da aka tambaye shi ko shawarar sa za ta haɗa da janye ’yan sandan da ke tare da shi, Ndume ya ce shi ba shi da wannan matsala.

Korafin dan majalisa kan janye 'yan sanda

A wani labarin, kun ji cewa wasu ’yan majalisa sun fara korafin matakin janye ’yan sanda da Bola Tinubu ya yi umarni a yi.

Kara karanta wannan

'Yan Majalisa sun fara shiga matsala bayan Tinubu ya janye 'yan sandan da ke gadinsu

Hon. Ahmed Idris Wase ya bayyana cewa ’yan bindiga sun fara aikawa mambobin majalisar da saƙonnin barazanar garkuwa da su.

Tsohon mataimakin shugaban majalisar ya roƙi shugaba Tinubu da ya sake nazarin wannan mataki na janye ’yan sanda ga manya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng