Shugaban Izala, Bala Lau Ya Tuno irin Haduwarsu da Marigayi Sheikh Dahiru Bauchi
- Shugaban Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana yadda suka yi mu'amala da marigayi Sheikh Dahiru Bauchi kafin rasuwarsa
- A ranar Juma'a za a birne jagora a darikar Tijjaniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi bayan Allah SWT Ya karbi rayuwarsa a ranar Alhamis
- Da ya ke magana a kan rayuwar marigayin, Sheikh Bala Lau ya tuno lokacin da su ke haduwa ana barkwani ba tare da cin mutunci ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Bauchi – Shugaban kungiyar Izala ta kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya bayyana yadda alakar da ke tsakanin sa da marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Ya bayyana cewa duk da akwai bambancin fahimta ta akida a tsakaninsu, ba su cin mutunci ko kokarin tozarta juna idan an hadu a wurin taruka.

Source: Facebook
A wata hira da ya yi da DCL Hausa da aka wallafa a shafin Facebook, Bala Lau ya ce su kan zolayi juna ba tare da cin zarafin kowa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bala lau ya magantu kan Dahiru Bauchi
Sheikh Bala Lau ya bayyana cewa su kan hadu a wuraren taruka ko aikin hajji, inda su kan tattauna na lokaci mai tsawo akan abubuwan da suka shafi akida da addini.
Ya ce:
“Allah Madaukakin Sarki ya karbi Sheikh Dahiru Usman Bauchi a wannan lokaci, kuma kowane rai zai dandani mutuwa kamar yadda Allah madaukakin Sarki ya tabbatar a cikin Al-Kur’ani mai girma. Kuma idan mutuwa ta faru, ana so ya zama darasi a kaskantar da kai, kuma a koma zuwa ga Allah Subhanahu wa ta’ala."

Source: Facebook
Ya kara da cewa duk da bambancin fahimta, ya zama tilas su yi ta’aziyya ga iyalansa tare da neman Allah Ya masa rahama.
A kalamansa:
“Mu kan zauna mu yi maganganu da yawa na abin da ya shafi irin akida da mu ke kai, mu yi ta tattaunawa. Amma tattaunawa ba tare da gaya wa kowa bakar magana ko cin zarafi ba.”
Alakar Bala Lau da Dahiru Bauchi
Sheikh Bala Lau ya tuna cewa wani lokaci Sheikh Dahiru Bauchi ya fadi wasu maganganu a kansa, amma ya mayar da magana ta ladabi da taushin harshe.
Wannan al’amari ya sa Shehin ya aika aka kira shi domin yi masa karin bayani, wanda daga baya ya kara fahimtar juna tsakanin su.
Ya ce:
“Yana da barkwanci, zai yi zolaya. Duk lokacin da aka hadu zai ce ‘kai dan Izala,’ mu ce ‘kai dan Darika.’ Duk irin wadannan kalomomi ba tare da an ci zarafin kowa ba.”
Bala Lau ya jaddada cewa wata kungiyar addini kadai ba za ta iya yin komai ba; dole ne dukkan Musulmi su hada kai wajen samar da ci gaba da fahimta ba tare da cin zarafi ba.
Maganar Dahiru Bauchi kan rasuwarsa
A baya, kun ji cewa fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi, ya taba bayyana adadin shekarun da yake kyautata tunanin zai rayu — yana cewa zai kai har shekara 102 a duniya.
A wata hira da mai magana da yawunsa, Muhammad Daha Al-Azahari, ya yi da manema labarai yayin shirin jana’izar mamacin, ya ce Sheikh Dahiru Bauchi ya nanata masa wannan batu.
Daga baya, bayan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi, Al-Azahari ya ce an samu wanda ya tabbatar da cewa malamin ya faɗi haka, kuma ya rasu watanni kadan kafin ya cika shekari 102.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


