Malami: EFFC Ta Gayyaci Ministan Buhari Kwanaki bayan Cewa zai Yi Takara a 2027

Malami: EFFC Ta Gayyaci Ministan Buhari Kwanaki bayan Cewa zai Yi Takara a 2027

  • Tsohon ministan shari'a na kasa, Abubakar Malami ya tabbatar da samun gayyatar hukumar EFCC a yau Juma'a
  • Abubakar Malami SAN ya ce yana da cikakken niyyar amsa kiran da hukumar ta yi masa, yana jaddada biyayya ga doka oda
  • Sai dai duk da bayanin da tsohon ministan ya fitar, har yanzu hukumar EFCC ba ta bayyana dalilin gayyatar shi ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya tabbatar da cewa hukumar EFCC ta gayyace shi.

Rahotanni sun bayyana cewa babban gwamnatin tarayyan ya yi alkawarin amsa kiran hukumar ba tare da bata lokaci ba.

Tsohon ministan, Abubakat Malami
Tsohon ministan Buhari da EFCC ta gayyata. Hoto: Abubakar Malami, SAN
Source: Facebook

Malami ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a, inda ya ce bai da wani abu da zai ɓoye.

Kara karanta wannan

Guinea Bissau: Gwamnatin Tinubu ta faɗi halin da Jonathan ke ciki bayan ya maƙale

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanin Abubakar Malami kan gayyatar EFCC

Abubakar Malami ya jaddada cewa yana bin doka kuma yana goyon bayan gaskiya da hidima ga jama'ar kasa cikin rikon amana.

A cikin rubutunsa, Malami ya ce:

“Ina tabbatar da cewa EFCC ta gayyace ni. A matsayina na ɗan ƙasa mai bin doka da kishin ƙasa, ina sake jaddada aniyata ta amsa wannan gayyata.”

Ya kara da cewa yadda ya fito fili ya sanar da jama’a shi ma wani ɓangare ne na goyon bayansa ga gaskiya da rikon amana a harkokin gwamnati.

Haka kuma Malami ya yi alkawarin sanar da al’umma yadda al’amura za su ci gaba da gudana, yana mai cewa ya yi haka ne domin gudun yada jita-jita ko bayanan da ba su da tushe.

Tarihin aikinsa da manyan shari'o'i da aka yi

Malami ya yi aiki a matsayin Babban Lauyan Gwamnatin Najeriya daga 2015 zuwa 2023 a zamanin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

"Mun san su": Sanata Maidoki ya ba gwamnati zabi 2 kan kawo karshen 'yan bindiga

A lokacin aikinsa, ya jagoranci da dama daga cikin manyan shari’o’in gwamnati da suka shafi dawo da dukiyar da aka sace, sauye-sauyen yaki da rashawa, da kuma manyan hukuncin kotuna.

Punch ta rahoto cewa ya taka muhimmiyar rawa a muhimman shari’o’in da suka shafi zargin manyan laifuffukan kudi, rikice-rikicen kwangila da sauransu.

Abubakar Malami yayin hira da 'yan jarida
Abubakar Malami a wani lokaci da ya yi hira da manema labarai. Hoto: Abubakar Malami, SAN
Source: Facebook

Abin da ake jira daga hukumar EFCC

A halin da ake ciki, hukumar EFCC ba ta fitar da wani bayani kan musabbabin gayyatar Malami ko irin tambayar da take son ya amsa ba.

Babu wani cikakken bayani game da ko gayyatar ta shafi wasu daga cikin shari’o’in da ya jagoranta ko dai rahotanni dangane da dukiyar da aka kwato a lokacin aikinsa.

Jama’a na zaman jiran ganin yadda wannan gayyata za ta kaya, musamman ganin cewa Malami ya kasance mai tasiri a harkokin shari’a da yaki da almundahana a gwamnatin Buhari.

Malami zai yi takarar gwamna a Kebbi

A wani labarin, kun ji cewa tsohon Ministan shari'a na kasa, Abubakar Malami ya ayyana niyyar neman gwamna a Kebbi.

A sanarwar da ya fitar, Abubakar Malami ya caccaki gwamnatin APC da cewa ta gaza biyan bukatun al'ummar jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan da ake zargi da yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu zai kai kansa EFCC

Sai dai jim kadan bayan fitar da sanarwar, gwamnatin Kebbi karkashin gwamna Nasir Idris ta ce ko gezau game da takarar da ya ce zai yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng