Dahiru Bauchi: Gwamna Bala Ya Ayyana Ranar Hutu a Jihar Bauchi
- Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana ranar hutu domin mutunta marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi wanda aka sanar da rasuwarsa
- Mai girma Sanata Bala Mohammed ya ayyana Juma’a 28 ga watan Nuwambar 2025 a matsayin ranar hutu don girmama marigayin
- Hutun zai bai wa ma’aikata, dalibai da mabiyansa damar halartar jana’izar, tare da nuna girmamawa ga fitaccen malamin Tijjaniyya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya ba da hutu a jihar Bauchi yayin da ake jimamin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Gwamna Bala ya ayyana ranar Juma’a 28 ga Nuwambar 2025 da muke ciki a matsayin ranar hutu domin girmama Dahiru Bauchi.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mukhtar Gidado ya fitar a shafin Facebook a yau Alhamis 27 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan
Guinea Bissau: Gwamnatin Tinubu ta faɗi halin da Jonathan ke ciki bayan ya maƙale
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta'aziyyar Gwamna Bala ga iyalan Dahiru Bauchi
Tun farko, Gwamna Bala Mohammed ya mika sakon ta'aziyya a madadin gwamnatin jihar Bauchi domin jajantawa iyalan marigayin.
Gwamna ya tuna irin gudunmawar da marigayin ya ba al'umma wurin koyar da addini da kuma tarbiya ga Musulmi baki daya.
Ya kuma yi masa ruwan addu'o'i domin samun rahama a gobe kiyama da kuma ba iyalansa hakurin jure wannan rashi.
Gwamnatin jiha ta bada hutun jana'izar Dahiru Bauchi
Sanarwar ta ce hutun zai ba ma’aikata, dalibai da masu bibiyar marigayi damar halartar jana’izar cikin sauki.
Gwamnati ta jaddada tasirin Sheikh Dahiru Bauchi wajen yada ilimin Alkur'ani, tarbiyya, zaman lafiya da hadin kai, tare da jagorantar mabiya cikin nutsuwa.
Haka kuma an bukaci al’umma su yi addu’a ga marigayin, tare da tallafa wa iyalansa, dalibansa da dukkan mabiyansa a wannan lokaci na rashin babban jagora.
Sanarwar ta ce:
"Mai girma, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed CON, FNIPR (Kauran Daular Usmaniyya), Gwamnan Jihar Bauchi, ya ayyana gobe Juma’a, 28 ga Nuwamba, 2025 a matsayin ranar hutu a fadin jihar.
"Wannan sanarwa ta zo ne a matsayin girmamawa da karramawa ga marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ake sa ran gudanar da sallar jana’izarsa gobe Juma'a bisa tsarin addinin Musulunci."
Rahotanni sun nuna cewa dubban Musulmai za su taru a Bauchi a gobe Juma’a 28 ga watan Nuwambar 2025 domin jana’izar da za a yi da misalin karfe 3:00 na rana a garin Bauchi.
Dahiru Bauchi: Sheikh Kabiru Gombe ya yi ta'aziyya
An ji cewa Sheikh Muhammad Kabiru Gombe ya bayyana alhini game da rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, inda ya tura sakon ta’aziyya ga al’ummar Musulmi.
A cikin sanarwar da ya wallafa a kafar sadarwa, ya jajanta wa dangin Shehu Dahiru Bauchi, yana mai cewa rasuwar ta yi matuƙar girgiza al’umma saboda tasirinsa.
Shehin malamin ya roƙi Allah ya gafarta wa marigayin, ya ƙara masa rahama, sannan ya ba iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi da aka yi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
