Guinea Bissau: Gwamnatin Tinubu Ta Faɗi Halin da Jonathan ke Ciki bayan Ya Maƙale

Guinea Bissau: Gwamnatin Tinubu Ta Faɗi Halin da Jonathan ke Ciki bayan Ya Maƙale

  • Gwamnatin tarayya ta yi magana bayan tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya makale a Guinea-Bissau
  • Ma'aikatar harkokin waje a Najeriya ta ce Goodluck Jonathan ya bar Guinea-Bissau lafiya bayan rikicin siyasa
  • Jami’in ma’aikatar, Kimiebi Ebienfa, ya ce Jonathan ya tashi musamman tare da tawagarsa, ciki har da babban jami'in diflomasiyya, Ibn Chambas

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Bola Tinubu ta yi martani bayan makalewar da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yi a Guinea-Bissau.

An tabbatar da cewa tsohon shugaban, yana cikin koshin lafiya kuma ya bar Guinea-Bissau a yau Alhamis 27 ga watan Nuwambar 2025.

Jonathan ya bar Guinea-Bissau zuwa Najeriya
Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan. Hoto: Goodluck Ebele Jonathan.
Source: Getty Images

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, ya shaida wa manema labarai cewa Jonathan ya bar kasar a jirgi na musamman, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Majalisa ta tsoma baki da Jonathan ya makale a kasar da sojoji suka yi juyin mulki

Yadda sojoji suka kwace mulki a Guinea-Bissau

Wannan na zuwa ne bayan rigimar siyasa ta barke a ƙasar Guinea-Bissau wanda ya jawo hambarar da gwamnati da kuma cafke shugaban kasar.

Sojojin Guinea-Bissau sun sanar da cewa sun karɓi cikakken iko a ƙasar bayan kwanaki uku kacal da zaɓen ’yan majalisa da na shugaban ƙasa.

Rahotanni sun nuna cewa tun da safiyar ranar Laraba 26 ga watan Nuwambar 2025, aka ji karar harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa yayin da sojoji suka mamaye manyan hanyoyi.

Dakarun sojin sun karanta sanarwa daga Babban Hedikwatar Soji a Bissau, babban birnin kasar bayan sun gama kwace iko.

Yadda Jonathan ya makale a Guinea-Bissau

Wannan lamari na zuwa ne bayan faruwar juyin mulki a kasar wanda ya jawo makalewar manyan mutane da dama.

Ebienfa ya tabbatar da cewa tsohon shugaban ya bar ƙasar tare da tawagarsa, ciki har da sanannen masanin diflomasiya, Ibn Chambas, ba tare da wata matsala ba.

Kara karanta wannan

Abin da gwamnatin Tinubu ta ce kan juyin mulki a Guinea Bissau, ta yi gargadi

Ya ce:

“Tsohon shugaban kasa Jonathan yana cikin cikakkiyar lafiya kuma ya bar Guinea-Bissau.
"Ya tashi da jirgi na musamman tare da sauran ’yan tawagarsa, ciki har da Ibn Chambas.”

Shin mene ne Jonathan ya je yi Guinea-Bissau?

Jonathan ya je Guinea-Bissau domin wani aikin zabe, amma rikicin siyasa da ya kunno kai ya sa aka gaggauta tafiyarsa tun kafin kammala aikinsa.

Tun bayan barinsa mulki a shekarar 2015, Jonathan yana ci gaba da ba da gudunmawa wurin tabbatar da inganta demokradiyya a Nahiyar Afirka.

Ya sha zama wakili a kasashen nahiyar da dama musamman lokutan zaɓe domin tabbatar da an yi adalci yayin zaben saboda inganta dimokuraɗiyya.

Guinea-Bissau: Majalisa ta bukaci dawo da Jonathan

A wani labarin, Majalisar Wakilai ta bukaci gwamnatin Najeriya ta fara bin matakan diflomasiyya domin dawo da Goodluck Jonathan gida.

Jonathan da sauran masu sa ido kan zaɓe sun makale a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a jiya Laraba.

Kara karanta wannan

Bayan rushe ofishin kamfen Tinubu, gwamna ya magantu kan jita jitar barin APC

Sojoji sun karɓi iko, sun dakatar da zaɓe, sun rufe iyakoki tare da kafa dokar hana fita da daddare a fadin kasar Guinea-Bissau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.