Kungiyar Izala Ta Yi Magana, Ta Tura Sako ga Iyalan Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Kungiyar Izala Ta Yi Magana, Ta Tura Sako ga Iyalan Sheikh Dahiru Usman Bauchi

  • JIBWIS wacce aka fi sani da Izala ta mika sakon ta'aziyya bisa rasuwar fitaccen malamin darikar Tijjaniyya, Dahiru Usaman Bauchi
  • A wata sanarwa da kungiyar ta fitar da yammacin ranar Alhamis, ta yi addu'ar Allah Ya jikan Shehu, ya kuma ba iyalansa hakuri
  • Da Asubahin yau Alhamis ne aka tabbatar fa rasuwar Sheikh Dahiru Usman a wani asibiti a cikin garin Bauchi yana mai shekara kimanin 100

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - Malamai, shugabanni, kungiyoyi da sauran musulmi daga ciki da wajen Najeriya na ci gaba da alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Kungiyar Jama'atul Izalatul Bidi'a Wa Iqamatis-Sunnah ta kasa (JBWIS) wacce aka fi sani da Izala ta bi sahun masu alhini da mika sakon ta'aziyyar rasuwar Shehin Tijjaniyya.

Shehu Dahiru Bauchi da Bala Lau.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi da Dr. Abdullahi Bala Lau Hoto: Jibwis Nigeria
Source: Facebook

Kungiyar Izala ta wallafa sakon ta'aziyyar rasuwar babban malamin addinin musuluncin a shafinta na Jibwis Nigeria da ke kafar sada zumunta na Facebook.

Kara karanta wannan

Bayan birne shi a masallaci, Sheikh Abdullahi Pakistan ya yi magana kan Dahiru Bauchi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakon Izala ga iyalan Sheikh Dahiru Bauchi

A sakon, kungiyar Izala karkashin jagorancin shugabanta, Imam Abdullahi Bala Lau ta jajantawa iyalai da daukacin al'ummar Bauchi da Najeriya bisa rasuwar Shehu Dahiru.

Izala ta kuma yi addu'ar Allah Madaukakin Sarki ya ji kan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Ya garfa masa kura-kuransa, sannan ta roki Allah Ya ba iyalansa hakuri da dangana.

A sanarwar da Izala ta fitar da yammacin yau Alhamis, ta ce:

"InnalilLahi wa inna ilaihi raji'un.
"A madadin kungiyar Izala, Shugaba Sheikh Dr. Imam Abdullahi Bala Lau, na miƙa ta'aziyya ga ƴan uwa da iyalan Shehu Ɗahiru Bauchi da al-ummar jihar Bauchi dama ƙasa baki ɗaya, bisa rasuwar Shehu Ɗahiru Usman Bauchi.
"Allah Ka gafarta masa kura-kuransa, Ka bai wa iyalansa dangana. Ameen."

Duk da haka, shugaban Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya mika sakon ta'aziyya ta musamman bisa rasuwar Dahiru Bauchi a madadinsa da iyalansa.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin da suka halarci jana'izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Sheikh Abdullahi Bala Lau.
Shugaban kungiyar Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau Hoto: Jibwis Nigeria
Source: Facebook

Za a yi jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi

Ana sa ran a gobe Juma'a, 28 ga watan Nuwamba, 2025 za a yi wa Sheikh Dahiru Bauchi jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada a masallacinsa da ke Bauchi.

Tuni dai shirye-shiryen sutura suka yi nisa kuma iyalan marigayin sun tabbatar da cewa babban malamin Hadisi, Sheikh Shareef Saleh ne zai yi masa sallah kamar yadda ya yi wasiyya.

Sheikh Dahiru Bauchi ya rasu ya bar mata hudu da 'ya'ya kusan 100 da jikoki da 'ya'yan jikoki da dama, kuma da-dama daga cikin iyalansa sun haddace Alkur'ani.

Wani dan Izala kuma dalibin ilimi, Malam Aminu Ishaq ya shaida wa Legit Hausa cewa sun yi jimamin rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi kuma suna masa fatan samun rahama.

A cewarsa, duk da suna da banbancin akida, amma kowa ya san Dahiru Bauchi ya ba musulunci gudummuwa, yana mai yabawa kungiyar Izala da ta tura sakon ta'aziyya.

Kara karanta wannan

Allahu Akhbar: An yi jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi, an birne gawarsa a masallaci

Malamin ya ce:

"Duk wadanda kuka ji suna zage-zage jahilai ne, babu wani cikakken ahlussunnah da zai murna da mutuwa, yau ko gobe ne, kowa sai ya tafi. Mutum kamar Dahiru Bauchi, an yi rashi babba.
"Muna masa fatan Allah Ya karbi kyawawan ayyukansa, Ya yafe masa kura-kuransa, Ya kuma sanya shi a gidan Aljannah, Ameen."

Bukola Saraki ya mika sakon ta'aziyya

A wani rahoton, kun ji cewa Bukola Saraki ya bayyana alhini kan rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya bayyana a matsayin jagora a ilimin addinin Musulunci.

Tsohon shugaban majalisar dattawa ya yabawa malamin kan shekarun da ya sadaukar wajen koyar da Al-Kur’ani da Sunnah a fadin Najeriya.

Saraki Ya mika ta’aziyya ga iyalinsa, Sarkin Musulmai, gwamnatin Bauchi, mabiya Tijjaniyya da dukkannin Musulmai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262