Ana Jimamin Sace Dalibai, 'Yan Bindiga Sun Sake Yin Awon Gaba da Mutane a Neja

Ana Jimamin Sace Dalibai, 'Yan Bindiga Sun Sake Yin Awon Gaba da Mutane a Neja

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun sake kai harin ta'addanci a jihar Neja da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya
  • Tsagerun 'yan bindigan sun farmaki mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka a wani kauye da ke karamar hukumar Shiroro
  • Sun kuma yi awon gaba da mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba wadanda suka hada har da mata masu dauke da juna biyu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Neja - ’Yan bindiga sun kai wani mummunan hari a kauyen Palaita, gundumar Erena, karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

'Yan bindigan sun yi garkuwa da mutum 24, ciki har da mata masu juna biyu, a wata gonar shinkafa.

'Yan bindiga sun kai hari a Neja
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago Hoto: @HonBago
Source: Twitter

Tashar Channels tv ta ce wani mazaunin yankin ya ce maharan sun afkawa mutanen ne misalin karfe 2:00 na rana a ranar Laraba, a lokacin da jama’a ke cikin girbin amfanin gona.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga babban birnin tarayya Abuja, sun yi garkuwa da mutane

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Neja

Duk da cewa kauyen Palaita na da tazarar kusan kilomita biyar daga sansanin sojoji da ke Erena, ’yan bindigar sun tsere da wadanda suka yi garkuwa da su kafin jami’an tsaro su kai dauki.

A wani harin daban tun da safiyar ranar, wata tawagar ’yan bindiga ta kutsa kauyen Kakuru, shi ma a cikin gundumar Erena.

'Yan bindigan sun azabtar da wani makaho, suka kuma yanke masa hannun dama bayan sun karɓi wayar da yake rike da ita, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da labarin.

Maharan, wadanda suka iso kauyen kusan karfe 8:00 na safe, sun tarar da shi kaɗai a gida domin sauran mazauna kauyen sun tafi gonaki.

Rahotanni sun nuna cewa mutumin ya shaida wa ’yan bindigan cewa wayar ba tasa ba ce, ta maƙwabcinsa ce wanda ya tafi gona.

Hakan ya fusata su, suka kwace wayar sannan suka yanke masa hannun dama.

Kara karanta wannan

Bayan ceto dalibai 25, shaidanin ɗan bindiga ya shiga hannun jami'an tsaro

Yanzu haka ana bashi taimakon farko a wani asibitin magani na gargajiya da ke Kuduru.

'Yan sanda sun yi bayani

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ana ci gaba da kokarin ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

“A ranar 26 ga Nuwamba, 2025, da misalin karfe 8:00 na safe, an samu rahoton cewa wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da kimanin mutane 10 daga kauyukan Angwan-Kawo da Kuchipa a karamar hukumar Shiroro."
"Ana ci gaba da kokari domin ganin an ceto su.”

- DSP Wasiu Abiodun

'Yan bindiga sun kai hare-hare a Neja
Taswirar jihar Neja, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wannan hari ya zo ne kasa da mako guda bayan ’yan bindiga sun sace dalibai da malamai sama da 300 daga makarantar St. Mary’s Catholic School da ke Papiri, jihar Neja, a ranar Juma’a.

Gumi ya magantu kan sulhu da 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya kare kansa kan jagorantar sulhu da 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: 'Yan bindiga sun shiga jihar Kano, sun yi garkuwa da mata

Sheikh Gumi ya musanta goyon bayan ayyukan 'yan bindiga, inda ya ce masu neman a kama shi sun yi masa gurguwar fahimta.

Malamin addinin Musuluncin ya zargi wasu kasashen waje da taimaka wa 'yan ta'adda da makamai, yana mai cewa Najeriya ba da kungiyoyin 'yan bindiga take fada ba, da wasu kasashen ketare take yaki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng